Abba Ibrahim Wada" />

Shin Rashin Kokarin Barcelona Ne Zai Dawo?

Zaben Shugaban Barcelona

Ranar Talata kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sha kashi a hannun Sebilla da ci 2-0 a gidan Sebilla a wasan daf da karshe zagayen farko a Copa del Rey kuma minti 25 da fara wasa Jules Kounde ya fara ci wa Sebilla kwallo, sannan tsohon dan wasan Barcelona, Iban Rakitic ya kara ta biyu daga baya.
Rabon Barcelona da kamfar cin kwallo tun karawar da Juventus ta doke ta ranar 8 ga watan Disamba a filin wasanta na Camp Nou a Champions League kuma tun daga lokacin tana cin kwallo a kalla daya ko fiye da haka a duk karawar da ta yi.
Tun bayan da Barcelona ta sha kashi a hannun Juventus ta yi wasanni 16, wadda kan zura kwallo a kowanne sannan cikin karawar da ta yi har da a gasar La Liga da Champions League da Copa del Rey da kuma Super copa de Espana.
Barcelona za ta karbi bakuncin wasa na biyu na daf da karshe a Copa del Rey ranar 3 ga watan Maris har ila yau Barcelona wadda aka doke a wasan karshe a Spanish Super Cup za ta buga Champions League da Paris St Germain cikin watan nan na Fabrairu bugu da kari kungiyar wadda ba ta ci kofi ba a bara tana ta uku a kan teburin La Liga na bana.

Exit mobile version