Abba Ibrahim Wada">

Shin Real Madrid Za Ta Iya Lashe Kofi A Wannan Kakar?

Bayan da kungiyar Real Madrid take ci gaba da fuskantar kalubale a kakar bana, sakamakon ‘yan wasanta da dama na yin jinya wanda hakan yana daya daga cikin matsalolin da suka addabi kungiyar.
Masana suna ganin idann har kungiyar zaa ci gaba da fuskantar irin wadannan matsalolin abune mai wahala ta iya lashe kofi a kakar wasa ta bana saboda yadda abubuwa suke tafiya ba daidai ba sannan kuma wasanni suna sake yin yawa.
Real Madrid wadda take rike da gasar La Liga, ba ta kare kofinta na Spanish Super Cup ba a shekarar nan, an kuma yi waje da ita a gasar cin kofin Copa del Rey bayan karamar kungiyar Alcoyano ta doke ta a watan daya gabata.
Real Madrid  ta mayar da hankali ne yanzu kan lashe La Liga wanda take ta biyu a kan teburin wasannin bana da kuma gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da za ta kara da kungiyar Atalanta cikin watan nan na Fabrairu da ake ciki.
To sai dai da yawan ‘yan kwallon Real Madrid na fama da jinya da hakan zai iya zama barazana kan kokarin da take na ganin ta tsira da kofi a kakar bana duk da cewa kungiyar bata kokari musamman idan tana buga wasa da kana nan kungiyoyi.
A satin daya gabata likitoci suka yi wa dan wasa Sergio Ramos  tiyata a kafarsa ya kuma bi sahun masu jinya da suka hada da dan wasa Eden Hazard da Rodrygo da Dani Carbajal da kuma matashin dan wasa Fede balberde.
Ranar Talatar da ta wuce kuma Real Madrid ta kara da Getafe, inda ta samu nasara daci 2-0 kuma daman Albaro Odriozola da kuma Eder Militao ba su buga karawar ba saboda jinya sannan kimanin ‘yan kwallon Real Madrid 10 ne  ke jinya.
A kalla sau 38 ‘yan wasan Real Madrid guda 20 suka yi rauni a kakar bana mai cike da kalubale sai dai hakan ya samo asaline sakamakon kungiyar ba ta dauki dan kwallo ba a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021, kuma cutar korona ta kawo tsaiko da ta kai ana buga wasanni da yawa a karamin lokaci babu hutu.
Real Madrid wadda take ci gaba da fuskantar barazanar rashin nasara za ta fuskanci kalubale a watan Fabrairu, wadda za ta yi wasanni shida har da daya a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a bana.
Real Madrid ta kai zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai, sai dai tana ta biyu a teburin La Liga da maki 46  kuma Atletico Madrid ce ta daya mai kwantan wasa daya da tazarar maki 9 tsakaninta da Barcelona sai 6 da Real Madrid.
A cikin watan Janairu aka fitar da Real Madrid daga gasar Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey na bana wanda hakan yasa yanzu gasar La liga da kofin zakarun turai ne kadai gasar data ragewa kungiyar da zata iya lashewa.
Saboda haka ya zama wajibi Real Madrid ta saka kwazo a watan na Fabrairu, idan ba haka ba ta fuskanci kakar bana ba tare da ta lashe kofi ba kuma kungiyar ta fara wasan farko cikin watan Fabrairu ranar Asabar, inda ta ziyarci kungiyar Huesca a gasar La Liga.
Sannan kwana uku tsakani Real Madrid  ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Getafe a kwantan wasan tun na makon farko da basu buga ba sakamakon dage wasan da akayi saboda nisan da sukayi a gasar zakarun turai na kakar data gabata.
A dai makon wato ranar Lahadi Real Madrid za ta buga gasar La Liga a gida da kungiyar balencia a filin ta na Di Stefano sannan daga  nan ne Real Madrid za ta ziyarci Real balladolid a gasar La Liga ranar Lahadi 21 ga watan na Fabrairu.
Real Madrid za ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Atalanta domin buga wasan farko a zagaye na biyu a gasar Champions League ranar Laraba 24 ga wata sannan kungiyar za ta karkare watan Fabrairu da gasar La Liga da za ta karbi bakuncin Real Sociedad.
Wasannin da Real Madrid za ta kara a Fabrairu:
Ranar Lahadi 14 ga watan Fabrairu La Liga
Real Madrid bs balencia
Ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu La Liga
balladolid bs Real Madrid
Ranar Laraba 24 ga watan Fabrairu Champions League
Atalanta bs Real Madrid
Ranar Lahadi 28 ga watan Fabrairu La Liga
Real Madrid bs Sociedad

Exit mobile version