Ibrahim Garba Nayaya" />

Shin Taron Ranar Marubuta Hausa Na Duniya Ya Bar Baya Da Kura?

Kamar yadda aka sani wannan rana, muhimmiyar rana ce gare mu, domin a wannan rana marubuta na Hausa, har ma da manazarta da makaranta daga sassan duniya su na dafifi, domin halartar wurin wannan taro tun shekarar da aka fara, wato 2016, wanda mu ka yi a Kano.

Dukkanin wanda ya halarci taron, to wajibi ne a kansa ya shaidi irin abubuwan da ya amfana da su. Daga ciki; sa-da-zumunta tsakanin juna, kwankwadar ilimi daban-daban a fannoni na adabi daga bakunan manya-manyan malaman jami’o’i da kwalejojin wannan kasa, har ma da wanin wannan. Misali; abin da ya shafi dab’i da tallata littattafai a kafofin soshiyal mediya. Baya ga wadannan, akan yi bajekolin littattafai sabbi da tsoffi, wanda hakan zai bai wa mutum mallakar wadanda ya ji labarinsu a zamunnan baya. Doriya a kan wannan, akan samu kyakkyawar alaka da fahimta tsakanin masu mulki da marubuta. Wannan ke bai wa masu mulki damar fahimtar amfani da muhimmancin marubuci.

A wannan shekara, kamar yadda mu ka gani, mun gudanar da wannan taro a jihar Katsina, inda tun kafin wannan taro ake nada kwamitoci daban-daban, domin gudanar da taron cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Sai dai a wannan shekarar an dan samu matsalolin da ba a rasa ba, wanda na ke tunanin birbishinsu ya faro ne tun kafin rana taron. Amma samuwar wadannan matsaloli ba zai rushe kokarin wasu cikin kwamitin shirya wannan taro ba, domin sun yi rawar gani sosai wanda har wasu ke hasashen inda wadannan mutane sun janye hannayensu, to da fa an samu matsala tun farko, ko ma da taron ya gagara.

Dauki misalin Bilkisu Yusuf Ali, a ranar farko ba ta bar wajen taron ba sai da ta ga an kai kowa makwancinsa. Ina kyautata zaton ni da Al’amin Daurawa ne mutane na karshe da sai wajen karfe 1:00 da wani abu na dare aka kai mu. To, idan ba dan ita ba, wa zai kai mu?

Kafin na zo an nuna duk wanda ya zo zai yi rajista, sannan a hada shi da wanda zai kai shi masauki, kuma a ba shi abinci. Da zuwana na fi awa daya Ina neman masu yin rajista, amma ban samu ba. Ba maganar rajista, balle abinci, balle masauki. Lokacin da na zo, a duk ’yan kwamiti, idan ban da Bilkisu, Fadila, Abdulrahman, Danborno, Fatimiyya, Kankia da Daurawa, sai wasu masu motoci, babu wanda na gani bayan su. Na dai ji wasu na rawa a cikin dakin taron. Afuwan; hatta shi kan shi shugaban kwamitin taron neman shi aka yi aka rasa, kuma an yi ta kiran wayarsa, amma ba ta shiga.

Sannan an samu wasu matsaloli a batun ajandar rana ta biyu ma, an samu sauye-sauye, domin tun a farko aka yi latti, sannan aka rika shigo da abubuwan da babu su, ko kuma aka rika kara mu su lokaci. Misali, masu waka kwata-kwata mintuna 20 ne a ajandar, amma fa an sha kida da waka kusan ya ninka na wadannan mintuna.

Idan ka dawo kan karanta labari, wannan ba zai zama illa ba, domin taron da ma na masu bayar da labarin ne. Don haka, ni a fahimtata, karanta labarai na da muhimmanci a gaban manya, wanda mun bar zaman safe da cewar za a yi da yamma, da yamma ba a yi ba, da dare kuma sai abin ya koma wani abu daban. A lokacin dan da Nasir Wada (mai gabatarwa a taron) ya yarda da laifinsa, da na san an wuce wurin! Idan da Shugaba Na’auwa ya kwantar  da hankulan wadanda su ka fusata, da magana mai dadi, wallahi da komai ya wuce.

To, amma duk  ba a yi haka ba; kowa sai kara tabbatar da maganarsa ya ke. Karshe ita ma Sa’adatu Kankia ta zo da  nata fadan, wanda ba haka yakamata ba. Idan mu ka koma kan maganar Farfesa Malumfashi Ibrahim, ai ya fayyace ma na kirkira da kuma yadda marubuci ke kirkirar labari, wanda mafi yawa gaskiya ne; ko dai ya faru da shi ko ga waninsa, amma sai a kara wani abu wanda bai faru ba, kila ma ya shamakance tunani da hankali domin tabbatar da wani abu. Kenan kuskure ne babba a kira masu son karanta wannan labari da makaryata.

Matsalolin wurin kwana kuwa, ban tsammanin akwai wannan, sai dai tabbas an yi jinkiri wajen kai mutane masauki. Ni idan ka dauki misali; a hotel aka ba mu daki, Maikudi Hotel, kuma wuri ne mai kyau, wanda dole ne mu cigaba da ganin kokarin Hajiya Bilkisu Yusuf Ali, kamar yadda na fada a baya, ba ta bar wurin taro ba sai da ta tabbatar an kai kowa masaukinsa.

Sai dai batun da wasu ke cewa, idan mutum na da kishi ko da kansa zai nemi masauki da abinci. Kwarai haka ne, amma domin me ake yin rajistar? Shin ba don abinci da masauki da satifiket ba ne? Ni Ina ganin bai ma dace a kawo wannan maganar ba kwata-kwata.

Ni a shawarata Ina ganin tun yanzu yakamata a fara zama domin yin wani tsari na cigaba da wannan taro a duk shekara. Ni a karan-kaina Ina da shawarwarin da na ke kyautata zaton idan an bi su, to wannan taro zai dore insha Allah. Daga cikin shawarwarin nawa kuwa, Ina ganin zai fi kyau a kafa wata dunkulalliyar kungiya ta marubuta Hausa ta kasa, wadda za ta dinke dukkanin kungiyoyin da ake da su.

A karkashin inuwarta, sai a rika shirya Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya kenan. A tsarin da za a bi, sai a rika canja shugabanni duk bayan wasu ’yan shekaru, sawa’un biyu ko uku. Sannan a rika sanya tarukan a mabambanta jihohi. Duk jihar da za a je, sai a rika kafa ‘Local Organization Committee’ a tsakanin ’yan jihar, sannan a samar da tsari na kwamitocin shirya wannan taro duk shekara.

Har wa yau, a samu wani sarki cikin sarakunanmu masu martaba ya kasance shi ne uban wannan kungiya ta kasa, kuma duk jihar da za a je yin wannan taro, to ya kasance gwamnatin jihar ce ke da alhakin bayar da akalla kaso sittin na gudumawar wannan taro.

Sannan a ware wasu ranaku a duk shekara wadanda a cikinsu ne za a rika gudanar da wannan taro. Misali, a sanya kwanakin Good Friday zuwa Ester Monday ko wasu ranakun da aka san za a samu wata babbar makaranta da dalibanta sun tafi hutu, kuma hutun ya kasance na kasa ne gabadaya.

Sannan kuma taron ya kasance ya na da manufofi da tsarin karantar da marubuta da bi da matakai nasu daban-daban. Hatta wadanda ke ganin sun wallafa littattafai da dama. Na tabbata idan aka yi haka, to za a samu komai ya gudana kamar yadda ake so.

Da fatan Allah Ya taimake mu, Ya hade kawunan marubuta cikin gaskiya da amana, amin.

 

Nayaya shi ne shugaban kungiyar Nguru Writers’ Association of Nigeriaa (NWAN) daga jihar Yobe.

 

Exit mobile version