Shin Wane Ne Ya Danawa Kasashen Afrika “Tarkon Bashi”?
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Wane Ne Ya Danawa Kasashen Afrika “Tarkon Bashi”?

byCMG Hausa
3 years ago
Afrika

Jaridar The Guardian ta Birtaniya, ya fitar da wani rahoto a baya-bayan nan, da ya yi kira ga cibiyoyin bayar da bashi na yammacin duniya, su saukaka tsarin biyan basussukan da suke bin kasashe masu karancin kudin shiga, musamman kasashen Afrika. 

Wannan rahoton na zuwa ne bayan cibiyar Debt Justice ta Birtaniyar, mai bibiyar yadda ake bayar da bashi tsakanin kasashen duniya, ta bankado wasu alkaluma dake nuna cewa, basussukan da cibiyoyin kudi na yammacin duniya ke bin kasashen Afrika, ya rubanya wanda kasar Sin ke binsu har sau 3, haka kuma kudin ruwansu ya ninka na Sin sau biyu.

  • Daya Daga Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja: Dalilin Sakin Faifan Bidiyon Azabtar Da Mu – Barista Hassan

Tambayar a nan ita ce, shin wane ne ya danawa kasashen Afrika Tarkon Bashi?
Batun “Tarkon Bashi” wani abu ne da kasashen yamma suka kirkiro, bisa zargi mara tushe da suke wa kasar Sin da kakabawa kasashen Afrika bashi fiye da kima. Sai dai, sun tsallake tarin basussuka da kudin ruwa da cibiyoyin kudi na kasashensu suka laftawa kasashen na Afrika.
Karya fure take ba ta ’ya’ya. Yanzu ga gaskiya ta fito, amma kasashen masu neman haifar da kiyayya tsakanin Sin da aminanta na Afrika, kawai saboda kishin karbuwar da ta samu, sun yi gum.
Duk wanda ya je kasashen na Afrika, zai ga yadda kasar Sin ta taimaka wajen gaggauta samar da kayayyaki na ci gaban da kyautatuwar rayuwa, daga kayayyakin more rayuwa, zuwa zuba jari da samar da aikin yi da tallafin karatu da na lafiya da bunkasa cinikayya da kafa kamfanoni, har ma da dakarun wanzar da zaman lafiya da sauransu. Hakika in ma bashi ne, an gani a aikace, domin duk wani katafaren aikin ci gaba a kasashen, za a ga cewa mafiya yawansu, Sin ce ta aiwatar. Duk da dimbin bashi da kasashen yamma suke bin kasashen, ba a ga wani abun a zo a gani da suka tabuka ba.
Bayan barkewar annobar COVID-19, kasar Sin ta amsa kiran kungiyar G20 na saukaka lokacin biyan bashi ga kasashe masu karancin kudin shiga, inda kawo yanzu ta sassauta biyan sama da dala biliyan 1.3, wanda ya dauki kaso 30 na jimilar shirin. Wannan ya sa kasar Sin ta zama kan gaba wajen aiwatar da shirin. A don haka ne ma, cibiyar Debt Justice ta yi kira ga kasashen yamma su tilastawa cibiyoyinsu na kudi aiwatar da shirin kamar dai yadda Sin ta yi.
Ina laifin mai taimakawa da kasancewa da kai a kowanne yanayi? Kasar Sin ta kasance mai amsa kiran kasashen Afrika a ko da yaushe, mai nuna kulawa a gare su, mai kare muradunsu a dandalin kasa da kasa, mai kai musu dauki cikin gaggawa, haka kuma mai jansu a jiki da yayata gogewarta gare su. Wadannan kadan ne daga cikin dalilan da ya sa kasashen ke kara aminta da ita. Kamar yadda shugaban Nijeriya ya taba furtawa da aka masa tambaya game da bashin kasar Sin, kofarsa a bude take ga duk wanda ke son taimakawa kasarsa, kuma kasar Sin ta kasancewa mai taimaka mata cikin sauki ba tare da sharadi ko katsalandan ba. Kuma shakka babu, irin hakan ne ke kasancewa a wajen dukkan kasashen nahiyar. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Sojoji 2 Da Farar Hula 1 Sun Mutum A Wani Hatsarin Mota A Legas

Sojoji 2 Da Farar Hula 1 Sun Mutum A Wani Hatsarin Mota A Legas

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version