Shin ya ‘Yan Chadi suka ji da haramcin Trump?

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya kasar Chadi cikin kasashe 8 da aka harantawa ‘Yan kasar shiga Amurka saboda abinda ya kira matsalar tsaro da kuma rashin ba Amurka hadin kan da ya dace.

Shugaba Trump ya ce ya dauki matakin ne domin kare lafiyar Amurkawa daga hare hare. Sauran sabbin kasashen da aka bayyana sunayensu sun hada da Koriya ta Arewa da Benezuela.

Ra’ayi dai ya banbanta akan yadda mutanen Chadi suka dauki matakin na Donald Trump.

Wasu na ganin matakin bai dace ba musamman yanzu da kasar ke cikin yanayi na tabarbarewar tattalin arziki.

Wasu kuma na ganin Trump ya nuna kishin kasarsa, matakin da ya dace ita ma Chadi ta yi koyi da shi.

Exit mobile version