Shin Yakamata A Ba Wa Lampard Karin Lokaci A Chelsea?

Lampard

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Frank Lampard, wanda kungiyar ta kora a ranar Litinin ya bayyana cewa ya cancanta a bashi cikakken lokacin da zai mayar da kungiyar matsayinta da aka sani na jagora a gasar firimiya.

Chelsea ta kori Lampard ne bayan ya kwashe watanni 18 yana horas da kungiyar bayan rashin sakamakon wasanni mai kyau da kungiyar ta fuskanta a lokacin da yake aikin koyar da ‘yan wasan.

Tsohon dan wasan tsakiyar na Chelsea, mai shekara 42, ya bar kungiyar da ke matsayi na tara a teburin gasar Premier bayan a makon jiya ta sha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Leicester City sannan wasa daya kacal Lampard ya ci a cikin wasanni biyar da ya buga a baya a gasar firimiya.

Wasansa na karshe shi ne wanda ya buga da kungiyar Luton a zagaye na hudu na gasar FA ya kuma yi nasara da ci 3-1 wanda duk da wannan nasara shugabannin kungiyar basu sake bashi wata damar ba.

An nada Lampard ya ja ragamar kungiyar na tsawon shekara uku, lokacin da ya maye gurbin Maurizio Sarri a Stamford Bridge a watan Yulin shekara ta 2019 kuma da zuwansa ya bawa matasan yara da dama a kungiyar dama irinsu Tammy Abraham da Mason Mount wadanda har tawagar kasar Ingila ce ta gayyace su.

A shekararsa ta farko, kungiyar ta kare a matsayi na hudu a gasar Premier, ta kuma je wasan karshe na gasar cin kofin kalubale na FA sai dai yanzu kungiyar na fama da rashin nasara a wasanni takwas da ta buga a baya a gasar, kamar yadda suka yi fama a wasanni 23 baya.

A sanarwar da Chelsea ta fitar ta ce wannan shawara ce mai matukar wahala da suka yanke, kuma ba shawara ce da mai kungiyar da kwamitin gudanarwarta suka yanke cikin sauki ba sai dai sun yanke shawarar ne saboda babu yadda za suyi duba da halin da kungiyar take ciki a daidai wannan lokacin.

“Muna godiya ga Frank Lampard bisa nasarorin da ya samu a lokacin jagorancin kungiyar sai dai, sakamakon da muke samu da kuma kokarin da kungiyar ke yi ba ta kai yadda muke so ba, abin da ya sa kungiyar take tsakiyar teburi kuma babu alamar samun ci gaba”. In ji Chelsea

“Raba gari da gwarzo irin Frank Lampard ba abu ne mai dadi ba, amma bayan dogon nazari da tattaunawa an yanke shawarar a kawo sauyi domin bai wa kungiyar damar samun ci gaba da taka rawar da ta dace da samun sakamako mai kyau a kakar wasanni.”

Mai kungiyar, Roman Abramobich ya ce za a bar mutum-mutumin Lampard saboda yana da muhimmanci ga kungiyar duk da cewa an sallame shi daga aiki saboda ya bautawa kungiyar a lokacin da yake dan wasa.

“Wannan shawara ce mai matukar wuya da aka yanke, ba dan komai ba saboda ina da kyakkywar alaka da Frank Lampard kuma ina mutun ta shi saboda mutum ne wanda ya kafa tarihin da babu wanda zai iya gogewa a wannan kungiya,” in ji Abromabic.

Wasu daga cikin matasan ‘yan wasan kungiyar dai ba suji dadin halin da kungiyar ta shiga ba sai dai duk da haka ba suji dadin korar da aka yiwa Lampard ba wanda shine ya basu damar da babu wani mai koyarwa da ya basu.

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Gary Nebille, ya soki hukuncin da kungiyar ta dauka na korar Lampard inda yace yakamata a bawa mai koyarwar lokaci kamar yadda Manchester United suka bawa Ole Gunner Solkljaer.

Exit mobile version