Shin Ziyarar Da Nancy Pelosi Ke Shirin Kai Wa Taiwan Ba Takala Ba Ce?
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin ziyarar da Nancy Pelosi ke shirin kai wa Taiwan ba Takala ba ce?

byCMG Hausa
3 years ago
Speaker of the House Nancy Pelosi, D-Calif., reacts to the Supreme Court decision overturning Roe v. Wade, at the Capitol in Washington, Friday, June 24, 2022. (AP Photo/J. Scott Applewhite)

Speaker of the House Nancy Pelosi, D-Calif., reacts to the Supreme Court decision overturning Roe v. Wade, at the Capitol in Washington, Friday, June 24, 2022. (AP Photo/J. Scott Applewhite)

Ko shakka babu, burin Amurka shi ne tada hankalin duniya domin cimma wani muradi nata na kashin kai. Kuma dukkan alamu sun nuna cewa, sam ba ta kaunar zaman lafiya.

A ranar Juma’ar da ta gabata, shugaban Amurka ya bayyana cewa, kasarsa na girmama manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma ba ta goyon bayan ’yancin kan yankin Taiwan.

Sai dai har kullum, Amurkar kan yi amai ne ta lashe. Yayin da shugaban kasar ya bayyana haka tare da cewa hadin gwiwar Sin da kasarsa na da muhimmanci ga zaman lafiyar duniya, sai kuma aka ji shugabar majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi na shirin ziyartar yankin na Taiwan.

Wannan fa na zuwa ne bayan kasar Sin ta yi gargadi da babbar murya game da hakan. Har kullum, shugaban Amurka kan furta wani abu dake karfafa gwiwar alakar kasarsa da Sin za ta kyautata domin amfanin al’ummun duniya, amma kuma, sai ’yan siyasar kasar su furta ko aiwatar da wani abu da ya sabawa hakan. Shin babu fahimta ne tsakanin shugaban kasar Amurka da sauran ’yan siyasar kasar? Ko kuma wani salo ne na makircin Amurka?

Idan Amurkar ba ta sani ba, wannan yana kara zubar da kimarta ne a idon duniya. Domin a ranar Juma’a, duk da muhimman batutuwa da aka tabo, an yi tsammanin ganin kyautatuwar lamura da dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu, amma kuma batun ziyarar Nancy Pelosi, ya kawar da wannan tunani.

Duk inda Amurka ta shiga, ta tsoma baki cikin harkokinsu na gida, to ba a karewa lafiya. Ga misali nan na zahiri ana gani a kan Ukraine, lamarin da ba kasashen dake rikicin kawai ya shafa ba, har da na shiyyarsu da sauran nahiyoyi, kai da daukacin duniya.

Kasar Sin dai, ta yi gargadi game da rashin amincewarta da ziyarar ta Nancy Pelosi a yankin Taiwan. Taiwan, yanki ne mallakar kasar Sin, don hak duk wata hulda ta jakadanci ta kai tsaye da yankin, ya keta manufar Sin daya tak a duniya, da tubalin hadin gwiwar Sin da kowacce kasa, haka zalika, ya take dokokin huldar kasa da kasa. Bisa la’akari da hakan, duk wata alaka ta kai tsaye da yankin, abu daya yake nufi, wato takalar fada.

A bayyane yake cewa, burin Amurka shi ne kokarin ta da rikici a Sin, ta daidaita al’ummar kasar sama da biliyan 1.4 dake zaune lami lafiya, da hargitsa tattalin arzikinta da tasiri da ma karfinta a duniya, sannan za ta ja gefe ta bar Taiwan, hakarta ta cimma ruwa ke nan.
A nata bangare dai kasar Sin kamar kowacce kasa mai sanin ya kamata, burinta shi ne tabbatar da dunkulewar kasar cikin lumana, sai dai kuma, hakan ba ya nufin za ta kyale ana yadda aka ga dama da yankunanta. Ta kuma nanata cewa, za ta yi dukkan mai yuwuwa, ciki har da daukar matakan soji, domin kare cikakken ’yanci da iko da yankunanta.(Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Kwamishinan Yobe, Goni Bukar, Ya Rasu A Hadarin Mota

Kwamishinan Yobe, Goni Bukar, Ya Rasu A Hadarin Mota

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version