Shirin Cusa Ɗa'a Da Kishin Ƙasa: An Fitar Da Daftarin Yaɗa Kyawawan Ɗabi'un Farfaɗo Da Martabar Nijeriya
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Cusa Ɗa’a Da Kishin Ƙasa: An Fitar Da Daftarin Yaɗa Kyawawan Ɗabi’un Farfaɗo da Martabar Nijeriya

bySulaiman
2 years ago
Kishin kasa

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya karɓi daftarin yaɗa kyawawan ɗabi’u da cusa ɗa’a domin farfaɗo da martabar Nijeriya.

Da ya ke karɓar daftarin da aka tsara don cusa ɗa’a a zukatan jama’a, Idris wanda a cikin Disamba ya kafa kwamitin tsara daftarin mai mutum 10, ya ce Shugaba Bola Tinubu ne zai ƙaddamar da shirin a cikin wannan shekarar.

  • Za Mu Dawo Da Martabar PDP A Katsina — Kwamitin Riƙon Ƙwarya
  • Tinubu Zai Kori Ministocin Da Ba Su Da Kwazon Aiki – Hadiza Bala Usman

A jawabinsa yayin karɓar daftarin daga hannun Shugaban Kwamitin, Dakta Auwal Haruna, a ranar Talata a Abuja, ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙudiri aniyar zayyana kyawawan ɗabi’un da za a cusa ɗa’a a zukatan jama’a ba tare da la’akari da nuna bambanci ko fifita wata ƙabila ko matsayi ba.

Kakakin Yaɗa Labaran Ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, sh ne ya fitar da sanarwar bayanin bayan taron karɓar daftarin a gaban sauran ‘yan kwamitin.

Idris ya ce: “Shi muhimmancin Daftarin Ɗa’a da Kishin Ƙasa gwamnati ce a kan gaba wajen ɗabbaƙa shi.”

Abin Da Daftarin Ya Ƙunsa:

Ministan ya ce daftarin ya ƙunshi Alƙawurra Bakwai da Nijeriya ta ɗaukar wa ‘yan ƙasar ta, sai kuma wasu Ƙudirori Bakwai da ‘yan Nijeriya ya za su ɗauka wajen kare martabar ƙasar su.

Ya ce daftarin zai tafi tare da yin la’akari da irin ɗimbin yawan matasan da wannan ƙasa ke da shi, waɗanda ke rayuwa duniyar da ƙirƙire-ƙirƙiren fasahar zamani ke da tasiri a duniya.

A kan haka ne ya ce gwamnati ta ƙudiri aniyar tabbatar da cewa matasa za su ja ragamar ƙoƙarin bunƙasa ƙasar nan domin samun dauwamammen cigaba.

Ministan ya yaba wa ƙoƙarin da gwamnatocin baya su ka yi wajen haƙilon neman hanyoyin da za a bi domin magance sakwarkwacewar kyawawan ɗabi’u a zukatan ‘yan Nijeriya, ta hanyar bijiro da shirye-shirye daban-daban a baya, irin su “Nigeria: Good People, Great Nation”, “Change Begin With Me”, da sauran su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
Next Post
Bukatar Samar Da Tsaftatacciyar Adawa A Nijeriya

Bukatar Samar Da Tsaftatacciyar Adawa A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version