Shirin Da Muke Da Shi Na Bunkasa Kasuwar Shaikh Abubakar Gumi – Alhaji Sulaiman Bambahu

Exif_JPEG_420

A ranar Litinin ne 31 ga watan Disamba, Shugaban hukumar kula da Kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, wacce aka fi da kira da babbar Kasuwar Kaduna, Alhaji Sulaiman Garba Bambahu, ya kira taron manema labarai domin ya bayyana kalubale da kuma irin nasarorin da ya samu a hukumar tafiyar da kasuwan tun daga lokacin da ya hau kujerar shugabancin hukumar kasuwan zuwa yau, da irin shirin da hukumar na shi ke da shi na kara bunkasa kasuwar a wannan sabuwar shekarar ta 2019. Umar A Hunkuyi, shi ne ya wakilci LEADERSHIP A YAU JUMA’A, a wajen tattaunawar. A sha karatu lafiya:

Za mu son jin cikakken sunan Shugaban hukumar kasuwanni ta Jihar Kaduna?
Suna na Sulaiman Garba Bambahu,
A halin yanzun ka sami sama da shekaru uku a kan wannan kujerar, me za ka gaya wa masu karatunmu?
Alhamdulillah, kamar yanda aka sani ne a lokacin da muka zo nan mun taras da kalubale marasa iyaka, wadanda muka fahimci cewa, matukar muna son cin nasara, tilas ne sai mun kawar da wadannan kalubalen. Zuwan mu a nan mun taras da matsaloli na kudi, ga ba kudin ga kuma tulin matsaloli nan birjik, kwata-kwata abin da muka taras a cikin asusun kasuwar nan shi ne Naira 97,000, kacal, alhalin ga basuka da ake binmu, da farko dai ma’aikata suna bin kudaden albashi na watanni da ba a biya su ba cikakke, ga NEPA suna binmu sama da milyan 1.5, wanda shi ke a daliln hakan ne muka zo muka taras da babu hasken lantarki a wannan kasuwa na tsawon kusan shekaru biyu. Sannan hukumar tara kudaden haraji ta kasa ita ma tana bin wannan hukumar kasuwan bashin sama da milyan 2, ita ma hukumar kula da kafa kamfanoni ta CAC, tana bin bashin shekaru masu yawa duk ba a biya ta ba.
Ga dai matsaloli nan masu yawa, ita kanta gwamnati, akwai kudin da ya kamata a ce wannan kasuwar tana baiwa gwamnatin, amma an sami shekaru ba ta baiwa gwamnatin ko sisin kwabo. A nan, mun taras da gwamnatin Jihar Kaduna, tana bin wannan kamfani kusan Naira milyan 500. Sashen masu aikin tsaro, da sashen masu tsaftace kasuwa, duk an yi watanni ba a biyansu…
Kar ka ce na katse ka, mun san wannan kasuwa ta Shaikh Abubakar Mahmud Gumi, tana da shaguna har sama da dubu biyar, to ‘yan kasuwan ba sa biyan kudin hayan shagunan ne, ko me ya faru har ake bin wadannan basuka haka?
To abubuwa ne masu yawa suka faru, wadanda ba nufinmu ne a nan mu fara lissafo su ba, mu dai abin da muka zo muka taras kenan a nan, wanda kuma muka kuduri aniyar mu dora namu kokarin na ganin duk mun kawar da su. daga cikin matsalolin ma da nake gaya maka, akwai na’urar samar da hasken lantarki na wannan kasuwar, (Transformer), mun zo mun taras da ta sami matsala na shekaru, amma an kasa gyarawa, ga ma’aikata a wannan lokacin sam babu tarbiya, babu maganan tura ma’aikata karo ilimi da gogewa a kan aikin su, kai mun taras dai a wannan lokacin abubuwa suna gab da tsayawa cik, domin hatta hukumar samar da kudaden shiga ta kasa ta rigaya ta bayar da wa’adin kulle wannan kamfanin, saboda ba a biyan su harajin da ya wajaba. Sai da na tashi daga nan har Abuja, ni da Sakatare na, muka je muka zauna da su muka yi yarjejeniya a bisa alkawari, suka kuma amince suka ba mu lokaci. Su ma mutanan NEPA, haka muka zauna da su, muka yi wannan yarjejeniya a bisa alkawari, suka dawo mana da hasken lantarki a cikin wannan kasuwar.
Sannan mun zo mun iske ‘yan kasuwa suna biyan abin da ake cewa, ‘Serbice Charge,’ watau kudin aikace-aikacen da ake yi masu, kamar na hasken lantari, masu samar da tsaro, masu shara da makamantan su, suna biyan Naira 5,500 ne, kowannen su, da mai babba da mai karamin shago, wanda muka duba sai muka ga sam babu adalci a kan hakan. Shi ne sai muka bullo da sabon tsari na biyan wannan kudin, ta yanda kowa zai biya daidai gwargwadon girman shagonsa ne. To a nan ne fa muka sami tirjiya, wanda a sakamkon hakan, babu irin fitinar da ba mu gani ba, ta yau daban da ta gobe. Da farko abin da aka fara kwadaita mana shi ne, irin abin da zai shiga cikin aljihunmu in mun bayar da hadin kai, da aka yi ta kokarin hakan aka ga mu ba irin wadancan din ne ba masu halin kwadayi, sai aka sake salo, sai aka fara kawo mana hare-hare da kokarin tsoratar da mu, da hakan ma ya gagara sai aka koma da fitina. To Allah Ya taimake mu, ba mu da kwadayi, ba mu da tsoro, muka dage a kan abin da muke da tabbacin shi ne gaskiya shi ne adalci, har muka fito da wannan tsarin biyan na kudaden. To a kuwa sakamakon wannan sabon tsarin da muka kawo, a yanzun haka, tun daga 2017, kawo yau din nan, ba a taba samun ko da rana guda hukumar NEPA ta zo ta yanke mana wuta ba, a kan wai ba mu biya ta kudin wutar da muka sha ba. Hakan kuma ya ba mu yanayin da muka kara bunkasa wannan kasuwar, ta hanyar sanya fitullu ko-ta-ina, masu amfani da hasken rana, ko a wannan shekarar kadai, mun sanya irin wadannan fitullun sama da 100 a cikin kasuwar nan, har yanzun kuma muna kan yi ba mu fasa ba.
Mun kuma sanya na’urorin kashe gobara, a lokacin da muka zo kasuwar nan, ko da guda daya babu duk da girman wannan kasuwar da yawan al’umma da dukiyoyin da ke cikinta. A kasuwar nan mun taras ko da irin dan bokitin nan na kasa na kashe gobara babu, amma yanzun ga su nan duk inda ka kewaya, ga na’urorin nan ga bokitan nan barkatai. Mun kuma samar da yanayi na lafiya saboda yanda muka inganta tsarin lafiya da samar da ma’aikata da kayan aikin da suka dace a cikin wannan kasuwar. Ba mu taba batan watan biyan masu gadi da masu shara na kasuwan nan albashin su ba. Ban da ma hakan, a kai, a kai, mukan yi feshin kashe kwayoyin cuta a cikin kasuwar nan. To a baya da suke faman rikici da mu a kan sabon tsarin da muka fito da shi, sai kuma a yanzun suka ga fa’idan sabon tsarin namu, a nan kuma sai aminci da dankon sosayya ya kullu a tsakaninmu, suka ce, a da mun dauka kamar yanda ake yi ne a baya, a raba mu da dukiyarmu ba a kuma aiwatar mana da komai ba, shi ya sanya a baya suka ki amincewa.
To duk wadannan suna daga cikin kadan na irin kalubalen da muka zo muka taras a wannan kasuwa, da kuma irin nasarorin da muka samu.
To a yanzun da muka shigo wannan sabuwar shekara ta 2019, ko kuna da wasu kudurorin na kara inganta wannan kasuwar?
Tabbas akwai, batun wuraren ajiyar motoci da ababen hawa yana daya daga cikin matsalolin da muka zo muka iske a wannan kasuwar, a yanzun haka, akwai tsarin da gwamnati ke jiran mu kai mata, domin Mai Girma Gwamna, Nasir El-Rufai, ya yi mana alkawarin zai ba mu wannan ginin na KSMC, wanda manufarmu shi ne mu gina katafaren wurin ajiyar ababen hawa a wajen.
Akwai shaguna masu yawa a cikin kasuwar nan, wadanda suke a kulle, a baya kun rabar da su amma mutane ba su bude su ba, me ake ciki a kansu yanzun?
Abin da ke faruwa shi ne, yawancin ‘yan kasuwar nan sun mayar da irin wadannan shagunan wuraren ajiyar kayayyakin siyarwan su ne, ba wai babu masu su ne ba, kasantuwar a lokacin da aka tsara kasuwar nan, ba a yi tunanin samarwa da ‘yan kasuwan irin wadannan wuraren ajiyar kayan na su ba. kowace kasuwa kuwa tana da bukatar a samar mata da abin da ake kira da, ware house, wuraren ajiyar kaya. Wannan kuma yana daya daga cikin abin da muke son tunkara a cikin wannan shekarar, da wurin ajiye ababen hawa da kuma wuraren ajiyar kayayyaki irin wadannan na ‘yan kasuwan, har ma mun sami babban kamfanin da zai gudanar da wannan aikin, ya gina mana wadannan wuraren ya kuma tafiyar da shi har ya fanshe kudin sa ya dawo mana da kayanmu mu ci gaba da tafiyar da shi.
A karshe me za ka cewa ‘yan kasuwa, ganin cewa an shiga sabuwar shekara?
Abin da zan cewa ‘yan kasuwa shi ne, ina taya su murnar bukin Kirsimati da na sabuwar shekara, ina kuma kara yin kira a garesu, don Allah, a ci gaba da bayar da hadin kai ga wannan gwamnatin ta Nasir El-Rufai, da ta Baba Buhari, a ba su cikakken goyon baya saboda su dawo su ci gaba mana da kyawawan ayyukan da suka sa a gaba.

Exit mobile version