Shirin Freedom Network Zai Sama Wa Matasa Dubu 150 Mafita – Talban Gaya

Babban Jami’i mai kula da Jihohin Arewa, Alhaji Kamal Mustapha Talban Gaya, ya bayyana cewa,  shirin Freedom Network na kusantar da al’umma da Bankuna ta hanyar ajiye kudi ko karbar su a lungu da sako na fadin wannan kasa, zai sama wa dimbin Matasa sama da 150,000 a Arewacin kasar nan aikin yi.

Talban na Gaya, ya kara da cewa, idan Matasan Jihar Kano da na sauran Arewacin Nijeriya suka karbi wannan shiri hannu biyu-biyu, to kuwa babu shakka, kowace Jiha da ke Arewa za ta iya sama wa Matasa aiki da bai gaza kasa da dubu ashirin (20) a kowane Jiha, idan aka yi lissafin Jihohin Arewa za ka ga dubban Matasa ne za su samu aiki a wannan Kamfani na Freedom Network.

Haka zalika, ya shawarci Matasanu da su tashi tsaye wajen rungumar wannan sana’a ta kusanta jama’a da Bankuna, domin ba da kudi ko karba ba tare da doguwar tafiya zuwa Banki ba, domin tuni mutanen Kudu suka yi mana nisa a irin wadannan harkoki. Don haka, ka da mu bari a bar mu a baya, tun da dai wannan hanya ce ta samun kudin halal, mai kuma dauke da riba wadda za ta ragewa Gwamnati nauyi a kowane mataki.

Sannn ya kuma bukaci Hukumomi a kan taimaka wa Matasa da jarin wannan sana’a wacce ko wane Matashi zai iya yin ta, gwargwadon jarinsa, daga 10,000 zuwa sama da Miliyan daya.

Shi ma Manajan Darekta kuma Shugaban Kamfanin Freedom Network, Femi Omogbeni Gun wanda ke tare da Shugaban sashin Kamfanin Nicholas Ossai, ya bayyan cewa, babban burinsu shi ne, sama wa Matasan Arewa da Nijeriya baki daya kyakkyawar makoma, ta hanyar sama musu aikin yi daidai da zamani.

Saboda haka ne ma yasa suka zo Kano, bisa jagorancin Alhaji Kamal Mustapha Talban Gaya, domin horar da wadannan Matasa yadda wannan kasuwanci yake, sannan ya yaba wa mutanen Kano, da Gwamnansu da kuma Sarakunansu, bisa irin cigaban Kano na Zaman Lafiya da kwanciyar hankali, wanda suka yi suna wajen karbar baki da kuma karrama su a koda yaushe.

Exit mobile version