Connect with us

KASUWANCI

Shirin Gwamnan Bauchi Na Kyautata Wa Kananan Masa’antu Zai Kawo Ci Gaba Matuka –Salisu Mai Suga ALHAJI SALISU GARBA MAI SUGA

Published

on

Daya ne daga cikin manya-manyan ‘yan kasuwa a jihar Bauchi kuma jigo a tafiyar jam’iyyar APC a jihar. Haka kuma ya rike shugabancin kungiyoyin ‘yan kasuwa da daman gaske, ciki kuwa har da raba tallafi wa ‘yan kasuwa daga gwamnatin da ta shude (shugaban gamayya). A hirarsa da LEADERSHIP ya shaida yadda gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar ke da shiri a kasa na inganta rayuwa ‘yan kasuwa a jihar da kuma karfafa kananan masana’antu a fadin jihar. KHALID IDRIS DOYA ne ya rubuta mana hirar:
Ka gabatar mana da kanka?
Suna na Alhaji Salisu Garba Mai Suga

Shin a wanne hali ‘yan kasuwan Bauchi suke a hanun gwamnati mai ci?
Gaskiya mu ‘yan kasuwa a jihar Bauchi dole ne mu yi alfahari da gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar. dalilanmu na alfahari da shi kuwa su ne tun da ya zo a matsayin gwamnan jihar Bauchi bai taba sayen wani abu a wata Jiha ta daban ba; sai dai a kira mu ‘yan kasuwar jihar Bauchi mu kawo. Dukkanin irin nau’in kayyakin da zai sayo ba zai dauka ya kai wata jiha don a kawo masa kayyakin ba, duk kuwa da sabonsa da sauran ‘yan kasuwar wasu Jihohin, kasancewarsa ya yi rayuwa a Kano, Kaduna da Abuja ka ga ya san wasu da dama, amma duk da haka Bauchin ya sani. Komeye zai saye zai kiramu zuwa gidan gwamnati a bamu kwantiragin kawowa. Gaskiyar magana wannan ba karamin taimaka wa kasuwancinmu ya yi ba, kuma hakan na matukar karfafa mu sosai a hidimar kasuwancinmu. Don haka muke cike da alfahri da shi kan wannan babin.

Akwai shawarorin da kuka baiwa gwamnan ne don ganin kasuwanci ta habaka a fadin jihar?
Hasalima mu mun shawarci mai girma gwamnan jihar Bauchi, muka ce masa a gwamnatin baya ta Malam Isa Yuguda ta taimaki ‘yan kasuwa da rance, shi wannan bashin sam babu ruwa a cikinsa, ita gwamnatin ne ta ce za ta bayar da naira biliyan biyu, aka kai zancen majalisar dokokin jihar Bauchi kuma aka amince. a lokacin gwamnati ta bayar da naira miliyan 500 a hanuna domin raba wa ‘yan kasuwa a matsayin rance. Mun kuma raba kudin nan, ya taimaka sosai, sannan an kuma dawo da abun da ya kamata. A bisa haka ne muka baiwa mai girma gwamna mai ci a halin yanzu da ya yi makamancin wannan tallafin bayar da lumunin rancen wa ‘yan kasuwa. Kasantuwar a halin da ake ciki waje ya yi wani iri, wasu ‘yan kasuwan suna matukar bukatar agaji, idan ka duba sai ka samu kowani irin mai sa’a sai ka samu ya dan jijjiga don haka ne muka shawarci gwamna M.A da ya yi koyi da wancan alkairin da aka yi wa ‘yan kasuwa a tsohowar gwamnatin baya, ya bayar da wannan rancen wanda babu ruwa a cikinsa sannan kuma babu biya da wuri.

Shi wannan rancen da kake ta magana a kai ya yake ne kam?
Yadda wancan rancen yake yana taimakawa sosai wa ‘yan kasuwa, za a baka bashin ne na tsawon shekaru biyu, za kuma a baka kasa kudin gida 24, in an baka miliyan goma ne za a kasa shi gida 24 kowani wata ka bayar da kashi daya har ka samu ka biya kudaden lamuni na rance da aka baka a gwamnatance. idan aka yi hakan, wani watan ma sai ka ga yazo maka da riga, a karshe dole za a ka samu dan kasuwa ya mallaki wani abu domin gina kansa. Mun dai baiwa gwamna mai ci shawara kan wannan, kuma ya amince zai yi, idan aka samu wannan rancen a wannan lokacin kasuwanci a jihar Bauchi zai yi matukar fabakuwa.
Bayan wannan, wani abun da ya bamu sha’awa da mai girma gwamna wanda muke ganin za mu rike shi hanu biyu gamgam mun bashi shawari, ni na bashi shawari na shaida masa cewar gwamna ka taimaka wa masu sana’o’i da masu kananan masana’antu, misali akwai kananan masana’antu irin su gidan ruwa ‘Pure Water’, gidan sarrafa buredi, gidan wankin mota ‘car wash’, gidan wankin kayan sawa gasu nan dai ratata. na shawarce kan cewar yadda zai ba mu, mu ‘yan kasuwa bashin da babu ruwa a ciki su ma masu irin wadanna kananan masana’antun a basu rancen da babu ruwa a ciki, hakan zai sanya su dada rike jama’a saboda kasancewar za ka samu masana’anta daya mutum 15, idan ka je gidan buga bulok sai ka samu sama da mutum 20 suna aikin suna neman abincinsu a gidan, gidan wanki da guga haka, gidan sarrafa ruwa mai tsafta haka, abun dadinka da gwamna ya amince ya ce zai yi wannan.
Baya ga wannan, mun kuma fadi wa gwamna kan cewar akwai masu sana’o’i, wanda a da baya gwamnatin jihar Bauchi ta sayi mashin mai taya uku ‘Keke-Napep’ sama da dubu biyar ta rabar a matsayin bashi, wanda ake biyan kudinta kadan-kadan, wannan ma mun ce wa gwamna ya kwaikwaya ya kuma amince ya ce za a sayi keke mai tayu uku domin raba wa masu sana’ar, gwamnan ya ma ce idan aka sayo za a kasafta kudin kashi uku, kashi daya su biya sauran kashi biyun kuma a bar musu an yafe musu ‘wannan nasarace’. Sannan kuma masu Acaba ‘Okada’ bayan an yi irin wancan na Keke-Napep su ma ya amince duk zai tafi da su a sayo mashinan nan a raba wa jama’a kashi daya za su biyu bisa uku sauran kashi biyu za kuma a bar musu kyauta, wadannan ma idan suka samu jihar Bauchi kasawanci zai kara ingantuwa sosai.

Ya za ka shaida mana yadda yanayin kasuwanci ke tafiya a jihar Bauchi a halin yanzu?
‘Yan kasuwa a kowani wuri su suna tafiya ne da mu’amalar mutane, mun shaida wa gwamna mai ci cewar mu ‘yan Bauchi muna tsaka-tsakiya ne, ba mu iyaka ‘Boda’, mu abun alfaharinmu a hidimar kasuwanci a jihar nan ma’aikatan gwamnati, in aka ba su albashinsu aka biyasu sai su shigo kasuwa su yi sayayya mu kuma mu samu riba. A nan sai muka nemi gwamna ya yi wa ma’aikata adashen ‘yar gata wa ma’aikatan, wannan adashen shine a samu kaso daya bisa uku na albashin jihar Bauchi kowace ranar 15 ga kowace wata a sanya kowani mai albashi da mai amsar fansho ya je a bashi kashi daya bisa uku na albashinsa idan karshen wata ya zo sai a cire wannan kashi dayan da aka bashi daga albashinsa, hakan zai taimaka wajen rage wa ma’aikata amsar basuka masu cike da riba a cikinsu, wasu za aka samu basu san ka’idar amsar bashi mai ruwa a cikinsa ba, misali za ka samu ma’aikaci wata ta yi nisa babu abinci kuma babu kudi, idan ma’aikaci ya rasa yadda zai yi sai ya je ya karbi kwano ya nemi wadanda addininmu ba daya da su ba ya amshi rance mai ruwa alhali mu addininmu ya hana amsar wannan ribar, idan misali kwano din naira dubu 10 ne sai a bashi a kan kudi naira 18 shi kuma ya saida dubu 9 ya amshi kudi, ka ga ya amshi kaya bashi mai ruwa a naira 18 ya saida 9 ka ga ma’aikaci ya cutu domin dai ya samu wata ta kai karshe. A don haka ne muka nemi gwamna ya yi adashen gata wa ma’aikata idan ya yi musu haka ma’aikata za su samu walwala kuma kukan babu-babu zai ragu da yardar Allah a jihar Bauchi, muma ‘yan kasuwa hankalinmu zai kwanta sosai.

Idan muka juya kan harkar tsaro, kasan matsalar tsaro takan sanya kasuwanci ya ja baya yaya wannan lamarin a jiharku?
Mu dai in dai a fannin tsaro ne za mu daga hanu mu gode wa Allah ne, a cikin shekaru uku tun da wannan gwamnatin ta zo hankali kwance. Ka san da Bauchi aka fara Boko Haram a gwamnatin baya, Allah ya kawo aka kashe Boko Haram, amma da Allah ya so taimakon gwamna mai ci sai Allah ya mantar da zuciyar wadannan mutanen gaba daya daga jihar Bauchi, ba su ma zuwa jihar balle su daga mana hankali, wasu sun tafi wasu sun halaka, wasu kuma Allah ya cire musu son Bauchi ga iyayensu amma basu sha’awar Bauchi sun yi tafiyarsu, Allah ya tsare daman wannan shine barazana a garemu Allah ya kare.
A bangaren zamantakewa kuwa a jihar Bauchi ba mu fada da ‘yan uwanmu wadanda muka taso tare, haka muka taso muka gansu suna rayuwa a jihar Bauchi, wannan shine matsalar amma babu shi a yanzu, a harkar tsaro mu lafiya kalau a jihar Bauchi sai godiya.

Wasu shawarwari ne za ka baiwa gwamnan jihar Bauchi Barista Abubakar?
Shawarata ga gwamnan Bauchi ya janyo ‘yan siyasa a jikinsa, ‘yan siyasar nan kuwa babba da karami, ba maganar wancan jam’iyya da wannan jam’iyyar ya jawo kowani dan siyasa a jiki domin ci gaban jihar Bauchi don a samu nasarar ciyar da jihar Bauchi. Wannan shine babbar abun da ya kamata gwamna ya runguma a halin yanzu, tun da yake gwamna ya zo ya ce mana shi baya gaba da kowani dan siyasa to muna son mu gani a kasa dukkanin wata jam’iyyar siyasa ya janyosu a jiki.
Babu wata gwamnati a jihar Bauchi da muke ganin yana da cikakken dama a hanunta na ta sake maimaita wa’adinta a karo na biyu kamar gwamnatin Muhammad Abdullahi Abubakar, sai dai in ya ki ya koma, tun da aka kirkiri demokradiyya a jihar Bauchi babu gwamnatin da take da dama cikin sauki kamar wannan gwamnatin, matukar zai yi abu mai sauki zai koma, haka Allah ya yi masa wannan damar.
Duk inda muka samu dama mukan fadi masa duk wani zancen fushi a daina shi a jawo kowa jiki, daman wani fushin rashin babu ne ke kawo shi, ‘yan siyasar nan masu hayani a dawo da su a amshesu sai ka ga kowani dan siyasa ya watsar da wutar yakin nasa.

Dangane da aikace-aikacen raya jihar Bauchi me za ka ce?
Na kuma shaida wa gwamna cewar aiyukan da ya sanya a gaba sun yi yawa a jihar nan, na ce masa a yanzu dai ya hakura da kirkiro mana sabbin aikace-aikace na ce masa ya yi hakuri ya tunkari aiyukan da ya faro sai ya kai ga kammalawa, ya zamana lokacin yakin neman zabe indan muka fita mu rufe bakin kowani dan siyasar da zai iya bude baki, duk wanda ya daga mana hanu sai mu daga masa. Amma yanzu idan aka sake tono wasu aiyuka da dama sauran lokacinmu ba su da yawa sai ka ga mun zo mun samu kalubale a 2019, tun da yanzu a kowace karamar hukuma 20 da suke jihar Bauchi akwai aiyukan da gwamna ya faro a samu a karasa a budesu hakan zai bamu dama a zaben 2019 sosai. Fatanmu ya yi duk kokarin da ke gabansa a halin yanzu ya tabbatar da cewar ya kammala aiyukan da aka faro, sannan kuma kamar yadda na yi maku magana a baya lallai da bukatar gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar ya janyo ‘yan siyasar jiharsa a jiki domin a tafi tare, duk kuma wani dan siyasar da kishin jihar ne a gabansa ya kamata ya sauki hukar yakin nasa a hada hanu wajen guda domin kai jihar Bauchi mataki na gaba, fushi da hayani ba zai haifar wa jihar da komai ba, don haka ne muke fatan a kawo karshen hakan, kowani dan siyasa ya rungumi jihar a matsayin abun da ke sama da tasa bukatar, ya so ci gaban jihar fiye da ci gabansa, ya tabbatar da ci gaban jihar fiye da tasa ta kowace fanni sai ga jihar ta samu nasarar cillawa sosai.

Alhaji mun gode da lokacinka?
Nima na gode kwarai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: