Shirin Kaddamar Da Majalisar Sarakuna: Ganduje Ya Ba Da Umarnin Gyara Gidan Shattima

Mahaifin Kwankwaso

A cikin shirye-shiryen kama aikin Majalisar Sarakuna gadan-gadan, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya baiwa Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje na Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji, umarnin yi wa Gidan Shattima, gida mai dadadden tarihi gyara domin zama Ofishin Majallisar Sarakuna wanda ke da’irar Fadar Sarkin Kano.

Bisa wannan umarni, hakan na nuna shirye-shiryen kaddamar da wannan Majalisa, na kan hanya, kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta dora alhakin ayyukan Majalisar Sarakunan da saurana abubuwan da suke da alaka da harkokin Masarautun, kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar, Kano Abba Anwar ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau Juma’a.

A jiya Alhamis ne dai, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin gaggauta aikin gyaran fitaccen Gidan nan na Shattima, wanda tuni abubuwan da ake bukata na fara aiwatar da aikin, duk sun kankama a Ma’aikatar Ayyukan da Gidajen ta Jihar Kano.

“Ba wai kawai sake fasalin tsarin gidan ba, ina kuma fatan ganin an aiwatar da
ingantaccen aiki, wadda Majalisar Sarakunan za ta kasance mai cikakken kwarjinin da za a tabbatar da cewa, lallai wannan ita ce Majalisar Sarakunan Jihar Kano.”

A wani cigaban kuma, Gwamna Ganduje ya amince da nadin Arc. Nuraddeen Zubair Yakub, a matsayin Babban Manajan Hukumar samar da gidaje na Jihar
Kano da kuma Dakta Saleh Jili, wadda aka nada a matsayin Babban Sakataren Hukumar bayar da Agajin gaggawa ta Jihar Kano, sannan nadin nasu ya fara aiki ne nan take.

Kazalika dukkaninsu, Yakubu da Jili sun karbi takardun kama wannan aiki nasu, sannan Gwaman Ganduje ya bukace su da su yi aiki tukuru, domin tabbatar da kyakkyawan zaton da ake yi masu, ya kuma kara da cewa, “ku yi kokarin jajircewa kan wadannan ayyuka da kuka samu amincewa akansu.”

Sa’annan ya jaddada bukatar da ake da ita, na kara himmatuwa wajen amfani da
fasahohin zamani wajen gudanar da ayyukansu, domin cigaban Jihar Kano bakidaya. “Kuna sane da cewa, harkokin ba kamar yadda kuka sansu a baya suke ba, saboda haka wajibi ne ku kara jajircewa wajen gudanar da ayyukan da aka damka amanarsu ahannunku”, a cewar gwamnan.

Exit mobile version