Musa Ishak Muhammad" />

Shirin Kwana  Casa’in Na Arewa 24 Shi Ne Silar Haskawata —Jaruma Surayya Aminu

Tattaunawar WAKILIN LEADERSHIP A YAU LAHADI, Musa Ishak Muhammad Tare Da Jaruma Surayya Aminu Ta Masana’antar Kannywood.

Da Farko Zamu So Ki Fadawa Masu Karatu cikakken sunanki da kuma takaitaccen tarihinki.

Assalamu alaikum ni sunana Surayya Aminu, an haife ni a garin Ikeja da ke Jihar Lagos, amma na girma ne a garin Kaduna. Na yi karatun firamare dina, da na sakandire, da na Islamiyya duka a garin  Kaduna. A yanzu kuma ina karatuna na digiri a Jami’ar Open Unibersity da ke nan Kano. Wannan shi ne tarihina a takaice.

Ya Ya Aka Yi Ki Ka Samu Kanki A Cikin Wannan Masana’anta Ta Fina-Finai?

Eh to a gaskiya tun ina karama ina da buri na in ga ina (acting) kuma inga ina abubuwa irin wanda ‘yan fim suke yi. Babban dai abinda ya sa na shiga fim din Hausa shi ne saboda ina da sha’awar in karanta Mass Communication, to wannan burin kusan shi ne abunda ya ja ra‘ayina wajen shiga harkar fim. Kuma kamar yadda na fada maka ina shawa’ar harkar  fim tun ina karama hakan ne ya ja hankalina na fara fim din Hausa.

Kusan Mafi Yawan Jarumai Za ki Ga Suna Da Wani Tsani Da Ya Zamar Musu Silar Shigowa Cikin Wannan Masana’anta, Idan An Tambayi Jaruma Surayya Wa Ne Ne Take Ganin Shi Ne Tsaninta Na Shigowa Wannan Masana’antar?

Eh to gaskiya a garin Kaduna wanda ya zamar min tsani na shigowa harkar fina-finan Hausa shi ne Nura M. Sultan, a nan Kano kuma Nazir Adam Sale. Wadannan su ne tsanina kuma ina alfahari da su a kodayaushe.

Wanne ne fim dinki na farko a rayuwarki?

Fim dina na farko wani fim ne mai suna ‘Kanin Miji’ kuma irin fim din nan ne wanda ana-yi-ana-ci-gaba, wato series film a turance. To wannan dai kusan shi ne fim dina na farko.

Izuwa Yanzu Kin Yi Fina-finai Kamar Guda Nawa A Cikin Wannan Masana’antar?

Izuwa yanzu dai fina-finaina basu da yawa, saboda zan iya cewa ban dade da shigowa wannan sana’ar ba,amma duk da haka zan iya cewa na  yi fina-finai kamar guda biyar a cikin wannan masana‘antar izuwa yanzu.

A Cikin Wadannan Fina-finai Guda biyar, Wane Fim Ne Kika Fi So Kuma Kike Ganin kamar Shi Ne Ya Fito Da Ke Duniya Ta Fara Saninki?

Gaskiya fim din da na fiso kuma wanda ya zama silar haskawata a duniya shi ne shirin Kwana Casa’in na Tashar Arewa 24, shi ne wanda ya haska ni sosai kuma gaskiya na fi son shi a cikin dukan fina-finan da na yi.

Ya Za Ki Iya Bayyana Yadda Kika Samu Kanki A Cikin Wannan Shiri Na Kwana Casa’in Na Tashar Arewa 24?

A gaskiya na ji dadi sosai a lokacin da na samu kaina a cikin shirin Kwana Casa’in, kuma naji dadin irin fiowar da aka bani a ciki wato (role) irin na munafinci da rawar kai da sauransu,a takaice dai na ji dadin kasancewata a cikin wannan shiri babu abinda zan iya cewa sai godiya.

A Cikin Fitattun Jarumai Da Ake Da Su A Duniyar Fina-Finai Tun Daga Nan Kannywood Har Izuwa Sauran Masana’antu Na Fina-Finai Kamar Su Nollywood Da Bollywood, Wacce Jaruma Kike Kwaikwayo Ko Kuma Kike Da Burin Ganinki A Irin Matsayin Da Take Kai?

To a gaskiya ni bani da wata jaruma da zan ce ita nake kwaikwayo, kawai a kodayaushe ina yin kokarina da irin tawa baiwar da Allah ya bani. Sannan kuma ni bani da wata wacca nake burun ganin na kai matsayinta, ni in son samuna ne shi ne na zama a saman kowacce jaruma. Saboda haka ni bana hangen kowa, a kodayashe ni kaina na sani ba hangen wasu ba.

Ya Za Ki Bayyana Alakarki Da Daraktoci, Furodusoshi Da Kuma Sauran Jarumai ?

Alhamdulillah gaskiya ina da mu’amala mai kyau da kowa a wannan masana’anta tun daga daraktoci, har zuwa jarumai. A cikin Daraktoci ina da kyakkyawar alaka da Darakta Aminu S. Bono kuma yana bani gudunmawa sosai a cikin wannan masana’anta. Haka suma sauran Daraktocin da kuma Producers din duk muna da kyakkyawar alaka da kuma mutunta juna a tsakanina da su. Jarumai kuwa sai son barka domin kuwa bani da matsala da kowa, ina da kyakkyawar mu’amala da dukkanninsu.

A karshe me ne ne sakonki ga masoyanki masu kallon fina-finanki, musamman masu kallon shirin kwana casa’in na arewa 24 wanda a nan ne aka fi sanin Jaruma Surayya ko in ce Rayya kamar yadda kike a cikin shirin?

Na gode na gode sosai, a gaskiya ina ganin soyayya a duk inda na shiga. Babu abinda zan cewa masoyana sai dai in ce na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bar zumunci, Allah ya bar mu tare.

Mun gode kwarai da gaske.

Nima na gode.

Exit mobile version