Shirin ‘Kwana Casa’in’ Shi Ne Taurarona Abin Alfahari Na -Jaruma Umma Shehu Bamalli                           

Jaruma

Tattaunawar WAKILINMU, MUSA ISHAK MUHAMMAD Tare Da JARUMA UMMA SHEHU BAMALLI Ta  SHIRIN KWANA CASA’IN NA TASHAR AREWA 24.

Da Farko Dai Za Mu So Mu Ji Cikakken Sunanki Da Kuma Takaitaccen Tarihinki.

To ni dai sunana Ummalkahairi, amma an fi sani na da Umma Shehu Bamalli. An haife ni ne a cikin dangin Bamalli, a birnin Zariya da ke Jihar Kaduna. A Kaduna na girma, a Kaduna na yi komai nawa, har kuma zuwa lokacin da wani dalili ya dawo da ni garin Kano da zama. Wannan shi ne a takaice.

Ya Ya A Ka Yi Ki Ka Samu Kanki A Cikin Masana’antar  Fina-finai?

Ni na dade Ina mu’amala da ‘yan fina-finai, na fara mu’amala da su tun wajen 2009. Amma ban taba fitowa a wani fim ba duk da mu’amalar da na ke da su. Fim din da na yi na farko a rayuwata shi ne fim din Kwana Casa’in na tashar Arewa 24. Kafun shi wannan shiri, ban taba yin fim ba kuma bayan shi ban kara yin wani ba zuwa yanzu.

Ki Na Nufin Tun Bayan Shirin Kwana Casa’in Ba Ki Kara Samun Kanki A  Cikin Wani Fim Ba?

Aa ba wai samu ne ban yi ba, kamfanoni da dama sun kawo min tallar fina-finansu ni ce dai kawai bani da ra’ayin sake yin wani fim din ne.

To Ya Ya A Ka Yi Ki Ka Samu Kanki A Cikin Wannan Shiri Na Kwana Casa’in Na Tashar Arewa 24?

Kamar wasa na tafi motsa jiki, sai mu ka hadu da Darakta Aminu S. Bono. Shi ne kawai sai ya ke ce min ai kuwa akwai wani shiri kwana casa’in da za a yi, ya ce in zo za su saka ni a ciki.

Kamar Yadda Ki Ka Fada Cewa Ba Ki Taba Fitowa A Wani Fim Kafun Kwana Casa’in Ba, Ya A Ka Yi  Shi Darakta S. Bono yay Gayyato Ki Cikin Shirin, Ya Na Da Tabbas Din Cewa Za Ki Bayar Da Abunda A Ke Bukata A Cikin Shirin Ne?

Kamar yadda na fada ma ka a baya cewa na dade a masana’antar fina-finai, kuma Ina tare da jaruma Jamila Nagudu. To kusan duk lokacin da za ta fita wani aiki tare mu ke zuwa. To idan mu ka je mu na haduwa da daraktoci musamman shi Bono, to wasu lokutan ina gwada yin (acting) to hakan ne dai ya sa ya gayyato ni domin na gwada.

A Cikin Wannan Shiri Na Kwana Casa’in Kin Fito Ne A Matsayin Matar Gwamna Malam Adamu, A Lokacin Da Ku Ka Je Tantancewa Kafun A Fara Shirin Ke Kadai Ce A Ka Tsara Za Ki Fito A Wannan Fitowar Ta Matar Malam Adamu, Ko Kuma Ku Na Da Yawa Bayan An Tantance Ne Ki Ka Samu Nasarar Fitowa A Wannan Mataki?

Da ba ma shi ne (role) din nawa ba, da farko an tsara zan fito ne a matsayin manajan gidan marayu. Daga baya ne an zo a na dan yi min tambayoyi sai darakta Salisu T. Balarabe ya ce zan fi dacewa a matsayin Dr. Usaina matar Malam Adamu. To kasan idan Allah ya tsara kai ne za ka samu abu, to komai yawan mutane sai ka samu wannan abun da Allah ya tsara maka samu.

Bayan Kin Samu Kanki A Cikin Jaruman Wannan Shiri Na Kwana Casa’in Wanne Irin Farin Ciki Ki Ka Samu?

Gaskiya na yi matukar farin ciki sosai da sosai, kuma na godewa Allah.

A Lokacin Da A Ka Fara Daukar Wannan Shiri Ya Ya Ki Ka samu Kanki Duba Da Cewa Shi Ne Karo Na Farko Da Ki Ka Fara Fitowa A  Matsayin Jaruma?

Gaskiya na dan ji wani iri da farko, fargaba ta dan fara kama ni amma daga baya sai a mu ka gama aikin mu lafiya kalau.

Idan Na Fahimce Ki Ba A Samu Wata Matsala A Lokacin Aikin Ba Kenan?

Eh gaskiya ba a samu wata matsala ba domin kowa ya na matakin yadda na yi aikin, domin na yi kamar na dauki dogon lokaci ina (acting).

Shirin Kwana Casa’in Shiri Ne Mai Dogon Zango Wanda Za A Dauki Wasu Lokuta A Na Gabatarwa, Idan A Yanzu Ki Ka Samu Tallar Aikin Wani Fim Din Daga Wani Kamfani Za Ki Yi Ne Ko Dai Kin Hakura Ne Kawai Da Shirin Kwana Casa’in?

Gaskiya ba na ra’ayin yin wani fim yanzu saboda wasu ‘yan dalilai nawa.

Ko Za Ki Iya Sanar Da Mu Wasu Daga Cikin Dalilan?

Kawai dalilai ne da su ka shafe ni a karan kaina amma ba wata matsala bace ta daban.

Wasu Jaruman Da Yawa Da Ma Wadanda Ba Jaruman Ba Za Ki Ga Su Na Sha’awar Harkar Fim Sosai, Don Har Su Kan Saka Dukiyoyinsu A Cikin Wannan Harka, Ke Ma Ki Na Da Wannan Tanadin Na Shirya Fina-finai Ko Da Ba Ki Ci-gaba Da Fitowa A matsayin Jaruma Ba?

Kwarai kuwa ina da wannan tsarin, kuma in sha Allah idan na samu dama zan yi.

To A Karshe Me Ne Ne Sakonki Ga Daukacin Masoyanki Musamman Ma’abota Kallon Shirinki Na Kwana Casa’in?

Ina mika sakon godiyata na musamman ga masoyana, na gode na gode da irin kaunar da su ke nuna min, kuma Ina kaunar su sosai kuma ina alfahari da su. Na gode, Allah ya bar zumunci.

To Jaruma Umma Shehu Bamalli Mu Na Godiya Sosai Da Ki Ka Samu Damar Tattaunawa da mu.

Ni ma na gode sosai da sosai.

 

 

Exit mobile version