Shirin N-Power Da N-Power Na Yin Matukar Tasiri A Nijeriya

Sakataren ilimi na karamar hukumar Bakori Alhaji Sanusi Yusuf Tsiga a jihar Katsina ya ya yaba wa gwamnatin taraya tare dagwamnatin jihar Katsina bisaga shirin nan da suka kirkiro na N-power yana yin matukar tasiri a jihar Katsina da kuma Nijeriya baki daya.

Sakataren ilimi ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake yi wa ma’aikata na wucin gadi malaman makaranta da gwamnatin tarayya ta dauka tare da gwamnatiun jihar Katsina domin su ba da ta su gudummawa ta fannin ilimi bako na yara kanan da kuma matsakaita a duk  fadin jihar Katsina da Nijeriya baki daya.

Ya kara da cewar wannan shiri na gwamnatocin guda biyu sun kirkiro shi ne domin kara bunkasa harkokin ilimin boko a cikin jihohin Nijeriya bak idaya da cewar wannan shiri ya taimaki matasan Nijeriya a wajen rashin ayyukan yi, da yawa  ya rage masu zaman kashe wando, in ji shi.

Bisa wannan kudiri na fadada ilimi boko. Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari ta dauki malaman makarantar firame na wucin gadi wadanda za a rarraba a makarantun  firamarena birni da karkara jihar Katsina domin kawo wa malamai na dundundun sauki a wajen koyarwa.

Sannan ya ci gaba da bayanin bangaren makarantun sakandire gwamnatin jihar Katsina ta dauki malamai masu takardun shaida cewa sun kammala digiri mutum dubu biyar wandanda za a rarraba a makarantu sakandire domin su ma su ci gaba da bayar da ta su gudummowar.

Exit mobile version