Shirin Rikicin Kabilanci Da Addini:Me Ya Sa DSS Suka Kara Gargadi?

DSS

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Hukumar Tsaron Ta Farin Kaya (DSS) ta sake yin gargadi game da shirye-shiryen da wasu mutane da kungiyoyi, wadanda ba ta ambaci sunansu ba, ke yi na yin amfani da wasu lamuran dake haifar da rikicin kabilanci da addini a wasu sassan kasar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Dakta Peter Afunanya, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

Idan za ku iya tunawa, tun a ranar 11 ga Janairu ne Hukumar ta fitar da sanarwar shirye-shiryen da wasu masu aiki tare da sojojin waje za su yi don tayar da rikicin addini a duk fadin kasar.

Sanarwar ta nuna cewa Jihohin da aka kai wa harin su ne Sakkwato, Kano, Kaduna, Filato, Ribas, Oyo, Lagos da kuma wadanda ke Kudu maso Gabas.

Sanarwar ta ce an tsara shi ne, don haifar da rikice-rikice tsakanin addinai da kuma amfani da dakaru sojoji don kai hari kan wasu cibiyoyin bauta, shugabannin addinai, mutane da mahimman wurare masu rauni.

Afunanya ya ce, sabbin abubuwan dake faruwa game da fadakarwar sun nuna matukar kokarin da wadannan kungiyoyi ke yi na gurgunta zaman lafiyar jama’a. Ya ce mutane na cigaba da amfani da maganganun tunzurawa, rashin kiyayewa da rarraba kawunan jama’a, aikatawa da kuma hada kan ‘yan kasa da juna don ganin sun haifar da rikice-rikicen kabilanci da na addini.

“A karo na 16, ya yi gargadin wadannan abubuwan da su hanzarta barin ayyukansu na (shirya) ko kuma su fuskanci fushin doka.

“DSS tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da jami’an tsaro, za su dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa,” inji shi. (NAN)

Exit mobile version