Shirin Sabuwar Kumbotso: Za Mu Fara Bai Wa Masu Cutar Koda Maganin Gargajiya Kyauta – Hon Sulaiman

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Jagoran Majalisar Kansilolin karamar Hukumar Kumbotso Honarabul Sulaiman Muhammad dan Baba ya bayyana aniyarsa ta daukar nauyin masu fama da cutar koda a karamar hukumar Kumbotso ta hanyar amfani da maganin gargajiya domin taimaka wa jama’a musamman a irin wannan lokacin da cutar ke neman zama barazana ga kiwon lafiyar al’umma.

“Munyi dogon Tunani tare bibiyar masu harkar maganunuwan Gargajiya domin samun tabbacin wanda za muyi amfani dashi wajen duba masu wannan cuta a karamar Hukumar Kumbotso. Kuma alhamdullahi yanzu mun samu kwararre wanda zamu fara wannan aiki dashi.”

Honarabul Sulaiman Muhammad dan Baba yace yanzu haka mun zakulo wadanda za’a fara baiwa maganin, wanda kuma muna tabbatarwa da Jama’a cewa duk inda mai fama da wannan cutar yake a karamar Hukumar Kumbotso muna yi masa bushara da cewa ya kwantar da hankalinsa domin jirfin fiton al’umma tuni ya kammala shirye shiryen fara sauke wannan kabakin arzikin.

Hakazalika Shugaban Majalisar Kansilolin karamar Hukumar ta Kumbotso ya jinjinawa Shugaban karamar Hukumar Alhaji Hassan Garban kauye Farawa bisa yadda yake karbar kyawawan shawarwarin da muke bayarwa tare bada dukkan goyan bayan da ake bukata.

A karshe Sulaiman dan Baba ya bukaci al’ummar Kumbotso dasu kara himmatuwa wajen baiwa wannan  Gwamnati dukkan goyon da ake bukata, wanda zuwa yanzu ga dukkanin alamu kwalliya tayi kyan rufi Jama’a na ganin alfanun shirin sabuwar Kumbotso a karkashin jagorancin Alhaji Hassan Garban kauye Farawa.

Exit mobile version