Daga Ahmed Muhammed Danasabe,
An bayyana rashin isassun kayayyakin aiki a matsayin babban matsalar dake fuskantar shirin samarwa da matasa aikin yi ta musamman da gwamnatin tarayya ta bullo da shi, wato( Special Public Work) a fadin kasar nan.
Jami’i mai kula da shirin( Superbisor) a gundumar Ward D dake yankin karamar hukumar Lokoja, a jihar Kogi, wanda kuma yana daya daga cikin matasan da suka amfana da shirin na SPW ,Kwamured Musa Datti, wanda aka fi sani da Musa D Lincoln ne ya bayyana hakan, a yayin da yake zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU, a Jiya talata a garin Lokoja.
Ya ce wasu daga cikin ayyukan da suke aiwatarwa sun hada da share titunan unguwanni da kwatami da magudanun ruwa da feshi don kashe kwari da dai sauran ayyuka makamantansu, amma kuma rashin isassun kayayyakin aiki, a cewarsa na kawo musu cikas wajen gudanar da ayyukan.
Musa D Lincoln ya kuma kara da cewa yawan wadanda suka amfana da shirin ta SPW a gundumar Ward D sun kai kimanin Dari da Ashirin, inda ya ce yawancinsu matasa ne kuma maza da mata.
Jami’in shirin wanda ya kara da cewa shirin na watanni uku ne kacal,kafin gwamnatin tarayya ta sake dibar wasu jerin matasan na watannin uku, ya ce gwamnati zata rika biyansu naira dubu ishirin(#20,000) a kowa ce wata.
Ya ce, koda yake kawo yanzu gwamnatin ta tarayya bata fara biyansu ba, amma kuma akwai alamu zata biya su nan bada jimawa ba, domin acewarsa, an turo musu asusun banki ( Bank Account) daga banki.
A don haka Mallam Musa D Lincoln yayi kira ga gwamnatin tarayya data samar musu da isassun kayayyakin aiki irinsu adaidaita sahu( Keke Napep) da shebur da adda da tsintsiya da dai sauransu.
Idan za a iya tunawa, a shekara ta 2020 ne dai gwamnatin tarayya ta bullo da shirin samar da ayyukan yi ta musamman ga yan kasa mai suna Special Public Work inda ta diba mutum 1000 a kowace karamar hukuma 774 dake fadin Nijeriya, tana mai cewa shirin zai rage rashin ayyukan yi da dimbin matasan kasar nan ke fuskanta.