Mustapha Ibrahim" />

Shirin Tallafa Wa Dalibai Na GPE/NIPEP: Kano Ce A Kan Gaba, In Ji Wakilan Majalisar Dinkin Duniya

Babban Jami’in shirin tallafa wa dalibai mata masu bukatar tallafi a makarantun Firamare na yankunan Karkara (GPE/NIPEP), Alhaji Abdushakur Abba Nuhu, wanda ke wakiltar kasashe takwas tare da kungiyoyin jin kai da Attajirai masu kishin bunkasa ilimi da tallafawa dalibai, ya tabbatar wa da mane ma labarai  cewa, Jihar Kano ce akan gaba wajen samun nasara cikin jihohi biyar na kasar nan da suka samu shiga wannan shiri na GPE/NIPEP, kamar yadda wakilan Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana a gaban Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yayin da wakilan Majalisar suka ziyarce shi Kano.

Har ila yau, ya kara da cewa wannan shiri na GPE/NIPEP, shiri ne wanda ya kunshi taimaka wa tsarin ilimin bai-daya ta hanyar taimakawa daliban makarantun share makarantar Firamare (ECC) da dalibai da cibiyoyin makarantu da kuma horar da Malamai har su kai ga mallakar takardar shedar Malanta ta NCE, wanda a cikin wadannan abubuwa da aka lissafa a sama suna da yawa a alkalman da suka amfana da wannan shiri na GPE/NIPEP.

Abdulshakur, ya ce yara dalibai mata 41848 suka amfana cikin shekaru uku na wannan shiri a Kano, sai kuma makarantu 2,307 da suka amfana da dai sauran abubuwa masu  yawa na Malamai mata da sauransu domin tallafin ya tabo abubuwa da dama wanda suka amfana da bunkasa iliminsu da kuma bada ilimi ga dalibai da makarantu da cibiyoyi da makarantu a tsarin baiwa mata dalibai tallafi ya tanaji cewa kowacce yarinya ana bata 15,000 a kowane zangon karatu, wanda kowace daliba tana samun 45,000 a shekara, sannan kuma su ne dubban da suka amfana da shirin GPE/NIPEP a Kano.

Exit mobile version