Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata - Wakilin MDD
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD

bySulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
9 months ago
MDD

A ranar 23 ga Janairun 2025, za mu kaddamar da Shirin Bukatun Jama’a (HNRP) na 2025. Shirin ya shafi mutane miliyan 3.6 daga cikin wadanda suka fi fama da rauni a jihohin Borno, Adamawa da Yobe (BAY), inda ake bukatar tallafin Dala miliyan 910.2.

Shirin HNRP a Nijeriya na 2025, na da nufin tallafawa wadanda kalubalen rikice-rikice ya fi shafa a kasar da ke bukatar agajin gaggawa.

  • Dole Mu Bai Wa Matasan Nijeriya Dama A 2027 – Bafarawa
  • NAPTIP Ta Ceto ’Yan Mata 9 Masu Juna Biyu A Abuja

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya,  Muhammad Fall ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa,  “daga abin da ya shafi yin hijira da ke haifar da rikice-rikice zuwa wani yanayi, karancin abinci, da barkewar cututtuka, Nijeriya na ci gaba da fama da matsalolin da ke dagula albarkatu da ayyukan jin kai.”

Duk da haka, wadannan kalubalen suna ba da damar sake tunani, gyara, da daidaita kokarinmu don samun ingantaccen sakamako, mai tasiri da dorewa.

Fall ya ce, “tsarin HNRP na Nijeriya a 2025 tsari ne da aka samar da nufin magance wadannan rikice-rikice masu yawa. Kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 33 ne ke fuskantar matsalar karancin abinci, yayin da yara miliyan 1.8 ke fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki, da kuma milyoyin da suka rasa matsugunansu a fadin kasar.

“Rikicin da ke faruwa a Nijeriya ya samo asali ne daga rikice-rikice da suka shafi tabarbarewar tattalin arziki da sauyin yanayi. Jihohin BAY dai na ci gaba da zama kan gaba, inda mutane miliyan 7.8 ke da da bukatar agajin gaggawa.

“A lokaci guda kuma, bala’o’i masu alaka da sauyin yanayi, irin su mummunar ambaliyar ruwa na 2024, sun lalata gidaje, filayen noma, da muhimman ababen more rayuwa.

“A karshe, shirin yana kokarin raba hanyoyin samun kudi. Hanyoyin ba da tallafi, sabbin hanyoyin da suka hada da hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu da tsare-tsaren da gwamnati ke jagoranta, hakan na da matukar muhimmanci wajen cike gibin da ake da shi,” in ji shi

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Nazarin CGTN: Tsauraran Manufofin Amurka Na Shan Suka

Nazarin CGTN: Tsauraran Manufofin Amurka Na Shan Suka

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version