Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Shirin Zamanantar Da Cinikin Lemon Fata Ya Kusa Kankama A Kano – Na’alto

by Muhammad
January 13, 2021
in LABARAI
2 min read
Lemon Fata
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

An bayyana kyakkyawar aniyar shugabancin kungiyar ‘Yan Kasuwar Lemon fata ta Na’ibawa a Jihar Kano kan shirin zamanantar da sana’ar da cewa tsari ne da zai inganta tare da habbaka tattalin arzikin ‘yan Kasuwa. Jawabin haka ya fito daga bakin shugaban kungiyar ‘yan Kasuwar Na’ibawa ‘yan lemo Alhaji Muhammad Na’alto alokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa dake Kasuwar ‘yan lemo a Kano.

samndaads

Yace hada hannu tsakanin Gwamnati da ‘yan Kasuwa wani tsari ne da idan aka tabbatar dashi tare da inganta shi zai haifar cikakken yanayin habakar tattalin arzikin ‘yan kasuwarmu, ya ci gaba da cewa yunkurin da ake na zamanantar da tsarin sanar sayar dan lemon fata shi ne hanya daya tilo da zata magance yawaitar asarar da ‘yan kasuwar ke yi musamman wajen rubewar lemo kafin sayar dashi dag a masu bukata. Muna alfahari da irin hadin kan da wakilin al’ummar Karamar Hukumar Kumbotso a majalisar wakilai ta tarayya da kuma shugaban karamar Hukumar ta Kumbotso wadanda ke bamu cikakken goyon baya

Alhaji Muhammad Na’alto yace zuwa yanzu mun fara samun raguwar yawaitar asarar da ‘yan kasuwar ke dibgawa sakamakon horar da wasu ‘yan kasuwar da akayi guda ashirin hanyoyin zamanantar da wannan da sana’a domin kaucewa tsunduma cikin tabka asarar da alokuta da dama kan yi sanadiyyar durkushewar wasu daga cikin ‘yan Kasuwar.

Daga nan sai ya bukaci hukumomin da abin ya shafa ayi kokarin samar da wata fasahar zamani kamar yadda muke ganin a wasu kasashen inda ake sarrafa irin wannan shara ta koma abin amfani da ka iya zama dunkiya ga masu ita. Don haka sai ya bukaci ‘yan kasuwa da daukacin masu ruwa da tsaki dasu kara himmatuwa wajen tsaftace kasuwar musamman ganin tana ta’ammali da kayan marmari wadanda ke bukatar kulawa ta fuskar tsafta kwarai da gaske. Yace akwai bukatar ‘yan kasuwa su kara jin tsoron Allah a dukkan al’amaransu domin inganta kasuwancinsu.

A karshe ya hori ‘yan kasuwar da suyi kokarin rike amanar abokan cinikinsu, musamman masu kawo kayan marmari daga kudancin kasarnan, ta fuskar biyan su kudaden kayansu akan kari, yin hakan ne zai kara amintaka tsakaninmu da bakin mu.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

’Yan Sandan Kano Sun Bajekolin Barayi Da ’Yan Damfarar Waya

Next Post

NAF Ta Kara Fadada Ayyukan Yaki Da Ta’addanci A Katsina

RelatedPosts

Buba Marwa Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NDLEA

Buba Marwa Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NDLEA

by Muhammad
11 hours ago
0

Daga Abba Ibrahim Gwale, Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince...

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Yau Za A Yi Karon Batta A Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano

by Sulaiman Ibrahim
20 hours ago
0

 Jam’iyyu 11 ne za su fafata PDP Kwankwasiyya ta ce,...

Sojoji

Tsofaffin Sojoji Sun Nemi Karin Kudin Fansho

by Sulaiman Ibrahim
20 hours ago
0

Kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Anambra ta bukaci...

Next Post
Sama

NAF Ta Kara Fadada Ayyukan Yaki Da Ta’addanci A Katsina

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version