Daga CRI Hausa
Yau Talata, ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da aikin da gwamnati ke yi na rage talauci a kasar. Takardar na nuna cewa, kasar Sin tana son shiga shirin rage talauci na kasa da kasa, domin zurfafa muamalar kasa da kasa kan aikin. Bankin duniya ya kuma fidda wani rahoto dake cewa, shirin ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta fidda, zai taimakawa mutane miliyan 7.6 na kasashen da shirin ya ratsa su fito daga kangin talauci, da kuma fitar da mutane miliyan 32 daga matsakacin talauci.
Cikin takardar, an kuma bayyana cewa, bayan kafuwar Jamhuriyyar Jamaar kasar Sin, ya zuwa yanzu, shekaru 70 da suka wuce, cikin wadannan shekaru 70, kasar Sin ta ba da taimako iri daban daban ga kasashe da kungiyoyi sama da 160, dake yankunan Asiya, da Afirka, da Latin Amurka, da Caribbean, da nahiyar Oceania da kuma Turai da sauransu, ta yadda, kasashe masu tasowa za su cimma burin neman ci gaba da MDD ta tsara.
A sai daya kuma, kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kasa da kasa wajen tsara shirye-shiryen rage talauci. A nahiyar Afirka, Sin ta ba da taimako ga kasashen nahiyar wajen gina ababen more rayuwa, da makarantun ba da horo, da kuma gina gidaje da sauransu, ta kuma kafa yankunan hadin gwiwar aikin gona, domin inganta hadin gwiwar fasahohin gona. Ban da haka kuma, Sin ta kuma kafa asibitin zumunci na Sin da Afirka, da hedkwatar rigakafin cututtuka ta Afirka da dai sauran makamantansu.
Bugu da kari, kasar Sin ta kafa wasu dandali, da shirya wasu darussan horaswa domin musayar raayoyi da fasahohi wajen rage talauci. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)