Khalid Idris Doya" />

Shirye-shiryen Gudanar Da Babban Zaben NUJ A Bauchi Ya Yi Nisa

NUJ

 

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Bauchi (NUJ) ta shirya tsaf domin gudanar da babban zaben sabbin shugabanni da za su jagoranci ragamar mambobinta na tsawon shekaru uku masu zuwa.

Wakilinmu ya nakalto cewar zaben zai gudana ne a ranar 22 ga watan Afrilun 2020, kamar yanda kwamitin shiryawa da gudanar da zaben su ka fitar.

Kawo yanzu gidajen rediyo, ma’aikatar sadatarwa ta jihar, talabijin da ita kanta sakatariyar ‘yan jaridun na jihar tare da wasu muhimman wurare sun cika sun batse  da  hotonan  ‘yan takara,  inda kowa ke neman a zabe shi tare da bayanin manufa da muradin da ya sanya ya ke/ta ke neman kujerar da take bukata dalewa.

Malam Umar M. Shira (BRC), shine shugaban kwamitin zaben, inda kuma Obed Ali Hassan (Ma’aikatar yada labarai ta jihar Bauchi) ya kasance sakataren kwamitin, a sanarwar da su ka manna a jikin allon talla da ke sakatariyar  NUJ,  Bauchi,  kwamitin sun shaida cewar zaben zai gudana ne  da  karfe  9  na  safiyar  ranar  22  ga Afrilu zuwa karfe 3 na yammaci.

Kwamitin sun  fitar  da  dokoki  da ka’idojin gudanar da zaben da suka kai guda 23 wadanda su ke son a bi domin tabbatar da yin zaben cikin nasara da kwanciyar hankali.

Wakilinmu ya nakalto muhimmai daga cikin dokoki da ka’idodin zaben da su ka hada da cewar dukkanin wadanda za su shiga takara a zaben sai mutum ya kai shekaru bakwai ya na aikin kuma wanda ya kasance cikakken mamba da kungiya ke amfana da shi.

“Dukkanin ‘yan takara dole ne su kasance masu rijista da uwar kungiyar NUJ ta kasa; har-ila-yau, sai mamban da ya ke da rijista da uwar kungiya ta kasa kuma yake da ‘Chapel’ nagartacciya ne zai iya dangwala kuri’a a yayin zaben.”

Kwamitin sun kuma baiwa ‘yan takara  zarafi  da  damar  yakin  neman zabe amma cikin kyakkyawar siga da kamala domin neman kuri’u daga mambobi, sai dai kwamitin sun haramta yakin neman zabe da bata kimar wani ko cin fuskar wani, “An  bude  yakin  neman  zabe  daga ranar 6 zuwa ranar 21 ga watan Afirilun 2020,” a cewar kwamitin.

Mambobin kwamitin zaben sun kuma ce, “Zaben zai gudana ne a tsakanin karfe 9am zuwa 3pm na ranar  Laraba  22  ga  watan  Afirilu. Za a fara kirga kuri’un zaben da aka kada nan take bayan rufe jefa kuri’u da karfe 3pm.

“Kowani mamba, ko wakilan ‘yan takara (Agents) ko ‘yan takara wajibi ne su nuna da’a a lokacin da zabe ke gudana,”

Kwamitin  sun  kuma  ce  kofar amsar korafe-korafe zai biyo baya kamar yanda tsarin zaben ya shirya, inda suka kuma ce za a kidaya kuri’u kana a sanar da wadanda suka lashe zabe a kowace kujera, inda kwamitin suka ce, wanda yake da rinjaye ne za a ayyana shi a matsayin mai nasara a kowace kujera.

Kwamitin zaben ya kuma ce, Chapel-Chapel za su tantance jerin mambobinsu tare da gabatarwa kwamitin, mamban da aka tantance daga Chapel dinsa ne kadai ke da hurumin shiga zaben. Kwamitin ya kuma haramta sayen kuri’u a lokacin zaben, sai dai an bada damar cewa ‘yan takara za su iya sayo dan abinci ga tawagarsu a ranar gudanar da zaben.

Kwamitin zaben ya ce, rantsar da sabbin shugabanni zai biyo bayan zaben ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba a ranar 22 ga watan Afirlun 2020. Shugaban kwamitin zaben Malam Umar M. Shira, da sakataren zaben  Obed  Ali  Hassan,  sun  fitar  da jerin ‘yan takaran  da  suka  tantance da sahalewa, wadanda za su fafata neman sa’arsu kan kujeru dabandaban, inda Bashir Idris (BRC) da shi  da  Umar  Sa’idu (Ma’aikatar  Yada labarai na jiha) za su fafata neman kujerar shugaban NUJ na jihar; a yayin da Abbas Maikano (NTA) da Hashimu U. Bulkwachuwa za su fafata neman kujerar mataimakin shugaba.

Sauran ‘yan takara sun kunshi; Isa  Garba  Gadau (Gidan Talabijin na jihar Bauchi) da Kabiru Garba (BRC) za su fafata neman sa’a a kujerar sakataren kungiyar; sai kuma a kujerar mataimakin sakatare (AS) ake da ‘yan takara uku, Bature Bala Malumfashi  (NTA), Adama  Ibrahim (Ma’aikatar Yada labarai ta jiha), da kuma Sani Mu’azu (Ma’aikatar Yada labarai ta jiha).

Sauran  kujerun  da  ‘yan  takarar da  ke  nema  sun  hada  da  Abubakar Musa Waziri (Globe FM) da Mohammad Inuwa (Globe FM) da za su fafata neman kujerar Ma’ajin kungiya.

Sai  kuma  kujeru  guda  biyu da babu masu hamayya na sakataren kudi wanda Najib Sani (Correspondents Chapel) ke nema, da kujerar Mai-Bincike (Auditor) da Danjuma S. Saleh (BRC) ke neman a zabe shi.

A daidai lokacin da zaben ke sauran mako guda a gudanar da shi, kawo yanzu ‘yan takara na ci gaba da gangamin yakin neman zabe.

Shugaban kwamitin zaben Umar Shira ya sha alwashin gudanar da zabe mai cike da gaskiya da adalci, inda ya nemi kowani mamban kungiyar ya kasance mai bin dokoki da ka’idojin da aka shimfida  domin  samun  nasarar gudanar da zaben cikin nasara.

Kwamitin zaben ya wallafa jerin sunayen mambobin da suke da zarafin  yin  zaben  da  yawansu  ya  kai ‘yan jarida 273 kawo yanzu.

Wakilinmu ya ce, yanzu haka NUJ reshen jihar ta na karkashin ikon kwamitin riko ne wanda Nasiru AbdullahiKobi (Gidan Talebijin din Bauchi) ke shugabanta tare  da  Bulak  Afsa  (NTA) a matsayin sakatariyar NUJ na rikon kwarya.

Exit mobile version