A yayin da yau Litinin ta farko a watan farko na Janairu na 2021, wanda ya rage saura kwana 10 ko awoyi 240 ko kuma minti 14400 kenan jama’ar Kano su hau layi, domin kada kuri’a, don zaben shugabanin kanana hukumomi 44 da kansiloli kimanin 484 da ke Jahar Kano yanzu haka dai a iya cewa hukumar zabe ta jihar (KANSIEC) ta yi nisa wajen tabbatar da nasarar zaben, kamar dai yadda Shugaban Hukumar zaben na Kano, Farfesa Garba Ibrahim sheka, ya tabatar wa duniya ta hanyar kafafen yada labarai a jihar.
Tuni sanya ranar zaben dai KANSIEC ta kama aiki ba dare ba rana, domin dai samun nasarar zaben, inda kuma tun a farkon wata gagarumar ganawarsa da manema labarai da hukumar ta yi ta fitar da jadawali na shirye shiryen da hukumar ta yi na aiki wanda ya hada da ranar da za su fara sayar da takardar neman tsayawa a takara ta kowane mukami da ya hada da na shugaban karamar hukuma da na matakin kansila ga dukkanin jam’iyun da suka amince za su shiga wannan zabe da lokacin da rakun tantancesu da dai sauran tsare tsare da Doka ta tsara ta amince da shi da za`a gabatar da shi na da awoyi 240 ida Allah ya kaimu lafiya
Har ila yau, sauran tsare-tsaren shi ne ziyarce ziyarce zuwa kafafan yada labarai da hukumin tsaro na kano sauran su ne Masarautun Kano biyar irinsu masarautar Kano, Bichi, Rano, Karaye, masarautar Gaya, sai kuma kananan hukumumi 44 da sauran tsare tsare wanda hukumar ke aiwatar cikin nassara kamar yadda dai KANSIEC ta tsara.
Haka kuma a wani labarin mai kama da wannan yanzu haka hukumar hana sha, da Fataucin mungan kwayoyi ta kasa NDLEA reshan Jahar kano karkashin shugabancin Dr Ibrahim Abdul ta fitar da wani bayani cewa bisa umarnin Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na a tantance dukanin wani da zai shiga takarar neman mukamin shugaban karamar hukuma ko kansila dan a tabatar ba a ba da dama ga masu sha, ko ta`ammali ta mugan kwayoyi sun shiga takarar ba, wanda yanzu haka hukumar ta tantance daukacin yan takarar, inda ta samu wasu daga cikin masu neman zama shugabanin kananan hukumumi da wasu masu neman zama kansiluli a kano inda NDLEA ta ce wasu daga ciki su na ta ammali da mugan kwayoyi duk da shugaban hukumar yaki da sha, da fataucin mugan kwayoyi na kano bai bayana suna su ba a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kano.