Kalu Eziyi" />

‘Shugaba Buhari Bai Da Wata kullalliyar Ajanda Kan Igbo’

Wani dan kabilar Igbo, kuma Jagora a jam’iyyar APC, Prince Benjamin Apugo ya yi nuni da cewa, tunanin da wasu ke yi da kuma wasu tsirarun ‘yan Nijeriya ke yi cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai da wata kullalliyar ajanda kan ‘yan kabilar Igbo.

Apugo, wanda ya kasance shi ne Yariman Ibekuland, ya bayanna hakan ne a yayin da da ya karbi bakuncin kwamitin jami’iyyar APC da ke sabunta katin ‘yan jam’iyyar da kuma yi wa wasu sabbin ‘ya’yan Jam’iyyar rijista a Jihar Abia.

Prince Benjamin Apugo wanda ya karbi kwamitin a gidansa dake a karamar Hukumar Umuahia ta Arewa da ke cikin birnin Umuahia ya kara da cewa, tun shigar Jamhuriya ta hudu a shekarar 1999, babu wata gwamnati da ta yi wa ‘yan kabilar Ndigbo adalci sai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, musamman wajen dada ‘yan kabilar ta Ndigbo kan manyan mukamai da kuma samar da ci gaba a yankinsu..

Benjamin wanda kuma jigo ne a uwar jam’iyar ta kasa ya kara da cewa, nada Majo Janar Leo Irabor, wanda kuma ya kasance dan kabilar Igbo da ya fito daga jihar Deltada shugaba Buhari ya yi, hakan ya kore tunanin da waau ke yi cewa, shugaba Buhari na da wata kullliayar ajanda kan ‘yan kabilar ta Igbo.

Da yake godewa kamitin kan ziyar, Benjamin ya kuma jaddada cewa, jamiyyar PDP a shiyyar Kudu Maso Gabas, na gab da bace wa, inda Benjamin ya kara da cewa, jamiyyar ba ta taba yin fatan alheri ga alumma ba.

Ya kalubalanci jamiyyar PDP dake a jihar wacce ya ce. Ta jima ta na rike da madadun ikon jihar, amma ta gaza samar da ci gaban alummar jihar.

Apugo ya kuma yi amfani da damar wajen yin kiwo ra ga ‘ya’yan jmiyyar da su yi amfani da damar wajen daidaita kawunansu domin dinke dukkan wata baraka don tunkarar zaben shekarar 2023, musamman domin a fafata da Jamiyyar PDP dake a shiyyar .

Shugaban kwamitin Jakada Bala Mohammed Mairiga a jawabinsa tundra farko ya danganta Apugo la matsayin daya daga cikin jigajigan masu ruwa da tsaki na jamiyyar a kasar nan, inda ya kara da cewa, hakan ne ya sa kwamitin ya yanke shawarar sake yin aikin rijitar a gidansa

Ya ce, aikin za a fara gudanar dashi a ranar Talata kuma ba an yi shi ne daga wata manufar fun zarafin ‘ya’yan jamiyyar ba, sai don kawai a bai wa ko wanne dan jamiyyar nasa yancin dangane da zaben shekarar 2023.

Exit mobile version