Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Da Masari Na Kara Karbuwa A Jihar Katsina

Published

on

Wani jigo na jam’iyyar APC anan jahar Katsina Sanata Abubakar Sadik Yar’adua ya fice daga cikin jam’iyyar APC akida.

Dangane da haka ne Alhaji Abubakar Sadik Yar’adua ya bukaci dukan magoya bayan shi su masa baya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamna Aminu Bello Masari.

Ya bada tabbacin neman karin magoya bayan da za su zabi shugabancin Muhammadu Buhari, da kuma gwamna Aminu Bello Masari a zabe mai zuwa.

Sanata Sadik na magana ne a taron gangamin magoya bayan jam’iyyar APC dake kananan hukuma goma sha daya na shiyyar dan majalisar dattawa ta Katsina ta tsakiya.

Sanata Abubakar sadik wanda ya shiga cikin sahun zaben fidda gwani na yan takarar a karkashin jam’iyyar APC ya bayyana aniyarsa ta dawowa daga rakiyar APC akida wadda ada shi ne shugabanta.

Ya shaidawa magoya bayanshi cewar sun warware rashin fahimtar dake tsakanin shi da gwamna wadda tasa suka kafa APC akida wanda yace dukkansa sun fahimci juna.

Sannan abokan siyasar sanata Sadik ne suka rura mashi baya a yayin rangadin daya gudanar.

Sun kunshi Alh. Musa Magaji wanda akafi sani da Musa Two Million, Hamza Rafin Dadi, dan Majalisar jaha mai wakiltar Dutsi Alhaji Haruna Aliyu Yamel da Gidado Lawal Bayawa.

Sauran sun hada da co-orinatocin kungiyar yakin neman na shi ne dake kananan hukumomi 34.

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Katsina Alhi Mamman Yaro Batsari shi ne ya jagoranci jami’an jam’iyyar a yayin rangadin.

Alh. Mamman Yaro rangadin da Sanata Sadik ke yi bata nufin cewar ya fito takara ne yana yi ne domin gangami ne na goyon bayan baya ga Shugaba Muhammadu Buhari.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: