Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Na Matukar Kokarin Kawo Canji A Nijerya –Ribadu

Published

on

Shugaba Muhammadu Buhari, yana kokarin kawo canji ne a kasar nan, don haka ana bukatar kowa ya bayar da na shi gudummawar wajen kawo canji mai ma’ana a kasar nan, kamar yadda tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, ya bayyana.

Nuhu Ribadu, ya bayyana hakan ne a garin Yola, ranar Asabar, a lokacin da yake shelanta aniyarsa ta neman tsayawa takarar gwamnan Jihar ta Adamawa.

Ribadu ya ce, “Buhari ya canza tsarin tafiyar da gwamnati a kasar nan, ta hanyar yin komai a bayyane kuma keke-da-keke a kowane sashe.

In har an zabe ni, ni ma hakan zan kwatanta wajen gudanar da gwamnatin a Jihar ta Adamawa.

A cewar sa, “Lokacin wawason dukiyar kasar nan ya wuce, a yanzun Nijeriya ta bude sabon babi ne da duk ‘yan kasa za su yi alfahari da kasar su.

Ribadu ya ce, bai kamata wannan canjin ya tsaya a mataki na tarayya ba kadai, kamata ya yi a ce duk Jihohi ma sun dabbaka irin wannan sauyin a gwamnatocin na su.

A cewar sa, “Ina neman mukamin gwamnan Jihar nan ne domin fatan da nake da shi na daukaka al’umman wannan Jihar kamar yanda kowa ya san ni da wannan aniyar a tsawon rayuwa ta duka. Hakan ne kuma ya kai ni ga shiga aikin tsaro a kasar nan, domin na yaki zalunci na kuma kawo ci gaba.

Da yake na shi jawabin, shugaban Jam’iyyar APC a Jihar ta Adamawa, Ibrahim Bilal, ya yi alkawarin cewa, Jam’iyyar za ta tabbatar da yin adalci wajen gudanar da zaben fidda gwani na Jihar.

Ya ce, duk wanda ya ci zaben a cikin ‘yan takaran uku, Jam’iyyar za ta goya ma shi baya har sai ya kai ga samun nasara.

“Na ji dadin yadda duk ku ka zo tarba ta, kun tudado da yawa cikin zafin rana domin ku yi mani maraba. Ba wani goyon bayan da za ku ba ni da ya wuce hakan.

“Hakan ya kara karfafa ni, yau mahimmiyar rana ce a gare ni, da duk ‘ya’yan Jihar nan masu neman ci gabanta, masu neman samar da shugabancin Jihar nan nagari.

“Na zo a matsayina na danku kuma dan’uwanku, tare da zimmar yi maku aiki da samar maku da ci gaba.

Na kwashe watanni ina ta yin nazarin yanda abubuwa ke gudana a kasar nan da kuma nan Jihar Adamawa. A matsayina na dan Jam’iyyar APC, kuma daya daga cikin wadanda suka taka mahimmiyar rawa wajen daukaka matsayin wannan Jam’iyyar, ina yin alfahari da abubuwa masu yawa da suka faru a wannan gwamnatin ta shugaba Buhari.

“Ina kuma ganin ya zama tilas ga duk ‘yan kasa nagari da su dafa wa shugaba Buhari a kan irin canji mai ma’ana da yake da shirin kawo wa a wannan kasar. Ba zai wadatar ba, a samar da canji a gwamnatin tarayya ta hanyar shugaba kwara daya tal mai gaskiya, dole ne a sami hakan a dukkanin sauran sassan gwamnati matukar muna fatan samar da ci gaba mai amfani da dorewa a wannan kasar.

 
Advertisement

labarai