Shugaba Buhari Na Murnar Shekara 30 Da Zama Angon Aisha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa kansa da iyalansa addu’ar neman zaman lafiya da albarka.

Shugaban ya yi wannan addu’a ne a shafinsa na Twitter, albarkacin cika shekara 30 da auren mai dakinsa Aisha.

A ranar Litinin 2 ga watan Disamba ne Shugaba Buhari da Aisha suka cika shekara 30 cif da yin aure.

Ita ma uwargida Aisha ba a bar ta a baya ba wajen wallafa sakon taya juna murna na wannan al’amari, inda a nata shafin na Twitter ta ce: “Mun gode wa Allah da cika shekara 30 tare.”

Wannan alama ce da ke nuna cewa ma’aurantan na zaune lami lafiya, ba kamar yadda a baya ake yayata cewa “akwai ‘yar tsama tsakaninsu ba,” musamman ganin yadda Aisha kan fito gaba-gadi ta fadi abin d ke ranta kan lamarin da ya shafi mulkin mai gidan nata.

Buhari da Aisha sun yi aure ne ranar 2 ga watan Disambar 1989 a garin Yola.

Allah ya albarkaci auren nasu da yara biyar da suka hada da Halima da Yusuf da Zahra da Aisha (Hanaan) da kuma Amina (Noor).

Suna da jikoki biyu tare da diyar Halima mai suna Aisha da kuma dan Zahra mai suna Ra’is.

Sai dai ba Aisha ce matar Shugaba Buhari ta farko ba, don kafin ita ya auri Hajiya Safinatu wadda ita ce matarsa ta fari. Amma sun rabu kafin daga bisani ta rasu.

Kuma sun haifi ‘ya’ya biyar da tare da suka hada da Zulai (marigayiya) da Musa (marigayi) da Fatima da Nana Khadija da kuma Safina (Lami).

 

Exit mobile version