Abubakar Abba" />

Shugaba Buhari Ya Ba Da Umarnun Raba Wa ‘Yan Nijeriya Shinkafar  Da Kwastam Suka  Kwace – Zainab    

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin a rabar da buhunhunan Shinkafa da aka yo dakon su a cikin motoci guda 150 da jami’an Hukumar hana fasakauri suka kama ga jihohin kasar nan  36.

Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan a taron  manema labarai a baban birnin tarayyar Abuja.

Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida  Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne kan matakan da Gwamnatin Tarayya take ci gaba da dauka don dakile bazuwar annonar cutar  Cobid-19 da kuma bayani kan farashin man fetur.

A cewar Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida    Zainab Ahmed, motocin da aka kwace dake dauke da Shinkafar yar kasa waje, an mika su ga  Ma’aikatar kula da walwalar jama’a  da magance aukuwar annoba don ta rabar da buhunhunan Shinkafar ga    yan kasar nan.

Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida  Zainab Ahmed ta ci faba da cewa, kari da wannan, Shugabankasa Muhammadu Buhari, ya kuma amince da a rabarda hasti   da za’a dauko daga rumbunan adana abinci  na Gwamnatin Tarayya dake a fadin kasar nan.

A cewar Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida    Zainab Ahmed, daga cikin irin kokarin da Gwamnatin Tarayya take kan yi na taimakawa manoman kasar   nan, Shugaban kasa Muhammadu Bugari ya kuma amince da yin ragin farashin takin zamani  daga nair  5,500 zuwa naira 5,000 nako wanne buhun takin zamani daya.

Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida  Zainab Ahmed ta sanar da cewa, wannan yana daya daga cikin matakan da aka dauka na samar da ragi ga manoman kasar nan idan akayi la’akari da irin illar da annobar ta COBID-19 ta janyowa tattalin arzikin kasar nan.

Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida Zainab Ahmed ta bayyana cewa, za’a dauki matakai da dama da zasu amfanun yan kasar nan..

Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida Zainab Ahmed ta sanar da cewa, baza mu yi gaggawar sanar da matakan ba.

A cewar Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida    Zainab Ahmed, burun mu shine muga ya zamu kara habaka tattalin arzikin  kasar nan.

Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida  Zainab Ahmed ta kara da cewa, gwamnatin zata ci gaba da daukar matakan da suka dace.

A karshe, Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida    Zainab Ahmed ta sanar da cewa, annobar ta yi tattalin arzikin kasashe da dama illa, inda, Ministar Ma’aikatar Kudi, Kasafin kudi da shirye-shiryen kasa Uwargida  Zainab Ahmed ta kuma kara hadda da  wasu matakai da  ake bukata  na magance kalubalen da ake fuskanta a yanzu a kasar nan.

Exit mobile version