Shugaba Buhari Ya Isa Birnin Sochi Na Kasar Rasha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bar birnin tarayya Abuja domin isa birnin Sochi dake kasar Rasha domin halartar taron kan kulla alakar ta tattalin arziki tsakanin kasashe Afrika da kuma Rasha.

Taron zai gudana ne a ranar 23 zuwa 25 ga watan Oktoba. Wakilan kamfanin dillancin labarai a fadar gwamnati da suke sanya idon akan tafiyar shugaban kasar, sun tabbatar da cewa shugaban kasar tare da tawagarsa sun isa babban filin jirgin sauka da tashi na Sochi da misalin karfe 11:25 agogon can wanda zafin yanayin ya kai digiri 22.

Magajin garin Sochi, Anatoly Pakhomov tare da tawagar jami’an gwamnatin Rasha ne suka tarbi shugaban kasar.

 

Exit mobile version