Shugaba Buhari Ya Nemi Jami’o’i Su Bankado Hanyoyin Kawo Wa Kasa Ci Gaba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci jami’o’in Nijeriya da su jajirce wajen bankado hanyoyin da za su tallafa wajen bunkasa ci gaban kasarnan.

Buhari ya yi wannan kiran ne a yau Asabar a garin Dutsinma da ke jihar Katsina a yayin da yake gabatar da jawabi a bikin yaye daliban Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma karo na hudu.

Shugaban, wanda tsohon gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya wakilce shi, a wani bangare na jawabinsa, ya ce; yanzu lokaci ne da jami’o’in kasarnan ya kamata su farka daga dogon bacci. Ya bayyana cewa; “bincike, zurfafa tunani, nazari tare da bankado sabbin abubuwa su ya kamata su mamaye tunanin jami’o’inmu, kamar yadda yake gudana a sauran jami’o’in duniya.” In ji shi.

Ya ce; ya kamata jami’o’i su zama wurare ne da suke bunkasa sabbin dabaru da za su bunkasa ci gaban kasarnan. Ya kalubalanci jami’o’in da kasawa wajen bankado hanyoyin ci gaba a kasarnan.

A na shi jawabin, mukaddashin mataimakin shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Baba-Kutigi, ya ce dalibai 430 jami’ar za ta yaye a wannan kakar karatu na 2017/2018.  Ya ce burinmu jami’ar shi ne kasance cikin jami’o’in da ake ji da su a duniya, inda ya ce a halin yanzu suna gudanar da darussa akalla 40. Ya ce ya zuwa yanzu Jami’ar ta yi Bankin ‘microfinance’, gonar Jami’ar, madabba’a tare da wurin siyar da kayayyaki domin samar da kudaden shiga.

Rahotanni sun nuna cewa; an ba da kyautuka ga daliban da suka zama zakaru.

Exit mobile version