Shugaba Buhari Ya Taya Sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Na 74 Murna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya taya dan Nijeriya wanda kuma shi ne sabon shugaban majalisar dinkin duniya na 74 murnar zabansa da aka yi a matsayin wanda zai jagoranci majalisar.

Shugaban kasar ya taya Ambassada Tijani Muhammad-Bande, murna ne a yayin da ya kai masa ziyara a ofishinsa dake birnin New York a kasar Amurka.

Wannan ziyarar ya biyo bayan taron majalisar da ake yi a kasar wanda shugaba Buhari na daga cikin wadanda suka halarci taron kuma zai gabatar da jawabi a wurin. Wanda taron zai fi maida hankali ne akan sauyin yanayi.

Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya tabbatar da cewa shugaban ya taya sabon shugaban murna bisa nasarar zabarsa da aka yi ya jagoranci majalisar na 74.

Exit mobile version