Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Ya Yaba Da Zuba Jarin Kasar Sin A Afrika

Published

on

Ranar Litinin ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna jin dadin sa ga kungiyar kawancen tattalin arziki ta Afirka ta yamma, (ECOWAS) a kan yadda kasar Sin ke kara sa hannun jari a kasashen kungiyar, da niyyar samar da jin dadin wani lokaci mai zuwa ga al’ummar kungiyar.
Shugaban ya yi wannan kiran ne lokacin da ake bude babban taron tsakanin Shugabannin Sin da kuma na Afirka,sai kuma wakilan harkokokin kasuwanci, a Beijin.
Ya yi bayanin cewar ita ce kasar wadda tafi sa jarinta a kasashen kungiyar, a gwamnatance da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, har ma shi al’amarin ya fara shafar wasu bangarori da suka shafi, samar da abubuwan more rayuwa harkar wutar lantarki, ga aikin gona, sai hakar ma’adinai da kuma bangaren kiwon lafiya.
Kamar yadda ya kara bayyana wa Sin har ila yau tana samar da taimako ta bangaren, da kuma jinkai da kuma al’amarin daya shafi canjin yanayi.
Ya ce, akwai ayyuka na gine gine wadanda ake yi a cikin kasashen kungiyar, da suka kuma hada da gina hanyoyin jiragen kasa wutar lantarki da kuma abubuwan more rayuwa fulaten jiragen sama da kuma hanyoyi duk ta hanyar taimakon kasar Sin.
“Ana iya cewar su mambonin kasashen na ECOWAS suna a cikin wani hali ci gaba don haka ziyarar da shugaban kasar China Di Jimping ya kawo, hakan yasa muka kara kaimi, saboda kara samun damar hadain kai sosai da sosai. Wannan kamar dai yadda ya bayyana ya zama dole “Saboda a kara samun sa hannun jarin Sin saboda abin ya taimaka ma kokarin da yankin yake na ci gaba da kuma dogaro da kai. “Ya kamata mu gane cewar, taimakon China yana da matukar muhimmanci saboda ita ce mai kara habaka tattalin arzikinmu, don haka akwai bukatar muma mu kara nuna dauriya da kuma nuna cewar da gaske muke”.
Ya kara jaddada cewar kasashen kawancen tattalin arziki na Afirka ta yamma ita ce ke da kashi 30 na yawan al’ummar Afirka, da kuma GDP, sun fara aiwatar da wasu tsare tsare, da kawo wasu manufofi wadanda za su kara karfafa ci gaban cikin gida na kasashen.
Shugaba Buhari ya bayyana cewar, su kasashen kungiyar suna kokarin kara inganta tattalin arzikinsu, inganta wasu tsare tsare da kuma manufofi, wadanda ana yin su saboda wani aji mutane wadanda mafi yawansu matasa ne saboda tabbatar da taimakon ya je gare su.
Don haka kamar dai yadda sai ya kara bayanai su kasashen kungiyar za su ci gaba da, ba sun kamfanonin da kuma ‘yankasuwar kasar Sin kwarin gwiwa, saboda su shigo su zuba jari a kasashen.
Bugu da kari ECOWAS za ta ci gaba da yin maraba da ‘yan kasar Sin su zo su ziyarci yammacin Afirka. Shugaban Nijeriya ya bayyana cewar yin hakan zai habaka “yanuwantaka mutum zuwa ga mutum” musamman ma yanzu yadda su kasashen suka maida hankalinsu ga al’amuran da za su kawo ci gaba.
“Kasashenmu Allah ya albarkace su da wuraren shakatawa masu kyau, tare da taimakon kasar Sin za a kara bunkasa harkokin shakatawa, ta hakan ne za a taimaka ma mutanen mu, samar da ayyukan yi ga al’ummarmu masu yawa, ta hakan ne za a rage fatara.”
Shugaban ya ne mi alfarma da a samar da biza ga ‘yan kasuwar nahiyar Afirka m,aza da mata, da kuma dalibai wadanda suke bukatar su kai ziyara Sin.
Ya bada tabbacin kasashen ECOWAS za su ci gaba da taimakawa, wajen bada muhimmanci, ga zuba jari daga kasashen waje a kasashen da suke cikin kawancen.
“Don haka muna sa ido musamman kasashen da suke cikin kawancen na tattalin arziki, suna jiran maganar al’amarin daya shafi wani tsari na shiga da fitar kayayyakin kasuwanci, saboda hakan zai taimaka masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da su samar wa kayayyakin su da kuma abubuwa da suke yi kasuwa a China.”
Buhari y ace irin wannan damar zata taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, na kasashen, daga dogara ga harkar noma da kuma ma’adinai.
Bugu da kari kuma ita damar idan aka same ta zata taimaka wajen gyara gibi na rashin daidaituwar harkokinn kasuwanci, tsakanin Sin da kuma kasashen ECOWAS ta yadda za a taimaka ma juna.
Yayin da yake nuna jin dadin sa akan yadda kasar China ta sa kanta cikin harkokin kasashen kawancen tattalin arziki na Afirka ta yamma. Shugaban ECOWAS har ila yau ya gode ma shugaban kasar Di Jinping, saboda alkawarin daya dauka na gina babbar sakatariya ta kungiyar.
Don haka ya kara bayyana daukar matakin da ECOWAS ta dauka, ta kara habaka wasu hukumomi a kasashen kungiyar,ta hanyar shugabanci nagari, yaki da karbar rashawa, maganin ta’addanci, kawar da tsattsauran ra’ayi da kuma al’amarin daya shafi aikata laifuka.
“Wandannan sune makaman da suka kamata a dauka saboda ci gaba da bunkasa tattalin arziki, na kasashen yammacin Afirka, idan har ana bukatar cimma burin”.
Advertisement

labarai