Shugaba Buhari Ya Yi Allah-wadai Da Harin ‘Yan Bindiga A Sakkwato

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Lahadi ya yi Allah-wadai da hare-haren ‘yan bindiga a Sakkwato. Inda ya nuna damuwarsa bisa kashe-kashen da ‘yan bindigar suka yi a wadansu kauyuka da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sakkwato.

Wannan sanarwar ta fito ne daga Kakakin Malam Garba Shehu in Abuja on Sua jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja. Inda ya tabbatar da cewa an sanar da shugaban kasar dangane da halin da ake ciki, kuma tuni ‘yan sanda suka kama wasu bisa zargin hannu a kai hare-haren.

Ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar, Aminu Tambuwal da ma al’ummar jihar baki daya bisa wannan hare-hare. Shugaban ya yi tir da wannan harin na ta’addancin akan wadanda ba su ji ba ba su gani ba, inda ya ce; tabbas wadanda suke da hannu za su fukanci fushin hukuma.

A karshe ya yiwa wadanda suka samu rauni addu’ar samun lafiya, inda ya ce gwamnati ba za ta gajiya ba wajen yaki da ta’addanci a kasarnan.

Exit mobile version