Ammar Muhammad" />

Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Olowo Na Owo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Oba Folagbade Olateru-Olagbegi, wanda shi ne Olowo na Owo da ma al’ummar Owo baki daya dake jihar Ondo bisa rasuwar wannan Sarkin mai daraja. Sakon ta’aziyyar ya fito ne ta hannu mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina a birnin tarayya Abuja a yau Alhamis.

Shugaban kasar ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen sarki abin koyi wanda ya hidimtawa al’ummarsa. Kuma ya bayyana shi a matsayin daya daga cikin mutanen da suka horas tare da ci gabantar da bangare lauya a kasarnan a lokacin da yake Malami a makarantar zama lauya ta Nijeriya.

Shugaban kasar ya ce za a ci gaba da tuna Sarkin a matsayin wanda ya ba da gudummawa bangaren zamantakewar al’ummar, ilimi da kuma bangaren tattalin arziki da zaman lafiya. Ya yi fatan samun Rahama ga Marigayi Oba Olateru-Olagbegi, wanda yake shi ne tsohon shugaban majalisar Obas ta jihar Ondo baki daya, tare da fatan samun wanda zai gaje shi ya yi koyi da shi.

Exit mobile version