Shugaba Buhari Ya Yi Tankade A Sashen Shari’a

A sakamakon shawarwarin da Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa ta bayar kan alkalan da aka zarge su da aikata laifuka a bakin aiki, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da korar Maishari’a O.O Tokode da kuma ritayar tilas ga Alkali Adeniyi Ademola, dukkansu alkalai a manyan kotunan tarayya.

Kafin yanke wannan hukuncin, Alkali Ademola ya yi alkalanci ne a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, yayin da shi kuma Maishari’a Tokode ya yi a Babbar Kotun Tarayya da ke Benin.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya raba wa manema labarai jiya a Abuja, ta bayyana cewa an dauki matakin ne bisa tanade-tanaden da ke sashe na 292, karamin sashe na 1, a karkashin sashe na biyu (b) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da aka yi wa kwaskwarima.

Sanarwar ta yi hannunka-mai-sanda ga sauran alkalan da ke bakin aiki inda ta ce: “Shugaban kasa yana kira ga alkalai su yi aikinsu bilhakki da gaskiya tare da kauce wa karbar cinhanci da rashawa a bakin aiki”.

Malam Garba Shehu, ya kuma fitar da wata sanarwa ta daban wadda ta bayyana cewa, “ana kan bin matakan tabbatar da cewa mutane, manyan alakalai da kanana da Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa ta aika sunayensu a nada su aiki a kotuna daban-daban sun cancanta, kuma ba su da wani nakasu a kan aikin alkalanci”. In ji sanarwar.

Malam Garba Shehu, ya yi bayanin cewa matakin da shugaban kasan ya dauka a kan nade-naden alkalan, karfin iko ne da sashe na 5 na tsarin mulkin shekarar 1999 ya bashi, wanda a karkashi aka bashi damar yin hakan tare da la’akari da duk abubuwan da suka kamata.

“Muna tabbatar wa ‘Yan Nijeriya cewa Shugaba Buhari zai nuna amincewarsa ko akasain haka da zarar an kammala tantancewa”.

Idan za a iya tunawa dai, a taron da Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa ta gudanar a ranar 6 ga Disambar 2017 ne ta ba da shawarar a yi wa Maishari’a Ademola da Maishari’a Tokode ritayar dole saboda nuna rashin da’a a aikin alkalanci.

Amma kuma majalisar ta ce, Ademola ya mika mata takardar sanarwar ritayarsa daga aiki tun a watan Oktoban 2017, sabanin ranar 9 ga Afrilun 2018, lokacin da ka’idar ritayarsa daga aiki za ta cika saboda ya cika shekara 65 yana aiki. Ta kara da cewa, ta ba da shawarar a yi masa ritayar dole ce a sakamakon binciken da majalisar ta yi game da zargin da aka yi masa a cikin takardar koken da wasu mutum takwas suka rubuta a kansa, a karkashin kwamitin ‘yanmajalisar wakilai na Jihar Anambara na jam’iyyar PDP.

Kwamitin mutanen ya zargi Maishari’a Ademola da nuna son-kai a wata shari’ar da ya yi kan zaben 2015 wanda ya gaggauta yanke hukunci saboda alakar jini da ke tsakaninsa da wanda ya kai kara•

Har ila yau, sun zarge shi da kin karanta wani sakin-layi daga cikin rubutaccen hukuncin da ya basu a gaban kotu kowa ya ji; tare da badda-bamin wata jumla, da masu koken suka nemi a sake duba su da idon basira a kotun daukaka kara lokacin da suka shigar da kara a gabanta•

Haka nan, sun ce akwai alamomin tambayoyi kan kwane-kwanen da maishari’an ya yi a cikin hujjoji da dalilan da ya bayar na hukuncin da ya yanke a kan shari’ar•

Bugu da kari, sun kuma zarge shi da kara yawan lokacin yanke hukuncin zuwa wata biyar maimakon wata uku da doka ta kayyade.

Duk da kasancewar masu koken sun janye zarge-zargen da suka yi wa Maishari’a Ademola, dokar ladaftarwa ta 16 ta Majalisar Harkokin Shari’ar, ta same shi da laifin kin yanke hukunci a daidai lokacin da aka ka’idance wanda yake nuna rashin da’a a bakin aiki. A cewar majalisar, wannan laifi ne bisa tanadin sashe na 292, karamin sashe na 1, a karkashin sashen na biyu (b) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Dangane da batun Maishari’a Tokode kuwa, Majalisar Kula da Harkokin Shari’ar ta ayyana cewa ta ba da shawarar a yi masa ritayar dole ne ba tare da bata lokaci ba, a sakamakon binciken da ta yi kan koken da Kungiyar Fafutukar Tabbatar da Rikon Amana da Gaskiya kan Sha’anin Kudi (SERAP), da kuma wanda Abimbola Awogboro suka gabatar mata.

Majalisar ta ce, masu koken sun zargi Maishari’a Tokode da karkatar da hankalin Hukumar Kula da Sashen Shari’a ta Tarayya da Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa, ta hanyar mika musu hukunce-hukuncen shari’o’i guda shida da ya yi ikirarin cewa shi ya yi a lokacin da yake aikin Lauya, a matsayin wani bangare na cika ka’idar nada shi babban jami’in shari’a kuma ya samu nasara aka nada shi.

“Sai dai kuma, daga bisani kwamitin binciken da majalisar ta kafa ya gano cewa shari’a daya ce kawai ya yi hukunci a kai daga cikin hukunce-hukuncen shari’o’i shida da ya mika”, in ji majalisar.

Bayan korar da aka yi wa Maishari’a Tokode, har ila yau zai amayo dukkan kudaden albashi da alawus-alawus da aka biya shi tun daga ranar 2 ga Disamban 2015 da aka rantsar da shi a matsayin Alkalin Babbar Kotun Tarayya har zuwa yau.

Wasu ‘Yan Nijeriya na ganin matakin da Shugaba Buharin ya dauka a matsayin kwakkwarar hanyar gyara sashen na shari’a ya dawo kan turbar kima da martabar da aka san shi da su tun tale-tale. Sannan za si zama izina ga masu ha’inci a cikin ayyukansu na shari’a.

 

Exit mobile version