Bello Hamza" />

Shugaba Macron Na Faransa Na Ziyarar Aiki A Afrika

Shugaban Faransa Eammanuel Macron na fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Afrika wadda za ta kai shi Mauritania wajen taron shugabannin Afrika kafin daga bisani ya isa Nijeriya.
Sanarwar da fadar shugaban da ke Paris ta bayar, ta nuna cewa shugaba Macron zai isa birnin Nouakchott ne a ranar Litinin, in da zai ci abincin rana da shugabanni da ke gudanar da taronsu na 31 a birnin.
Shugaba Macron zai yi jawabi kan muhimmancin rundunar G5 Sahel da ke yaki da ‘yan ta’adda wadanda kasashen Burkina Faso da Mali da Mauritania da Jamhuriyar Nijar da kuma Chadi suka bada gudumawar sojoji, kafin ya tashi zuwa Nijeriya yau Talata.
Yayin ziyararsa a Nijeriya shugaba Macron zai gana da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja, birnin da Macron ya yi aiki na watanni 6 a shekarar 2002, kafin ya zarce zuwa birnin Lagos.
Ana saran shugaban ya zama shugaban Faransa na farko da zai ziyarci Lagos, in da zai halarci dandalin Fela Kuti tare da rakiyar mawakin Senegal Youssou N’dour da Angelikue Kidjo ta kasar Benin, in da ake saran zai bayyana shirin gudanar da bikin al’adun Afrika da zai gudana a shekarar 2020 a Faransa.
Ana kuma saran Macron ya gana da matasa masu zuba jari a karkashin shirin bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Fadar shugaban ta ce, yana da matukar muhimmanci a sake fasalin labaran da ke fitowa daga Nijeriya, maimakon matsalar tsaro da fashin teku zuwa muhimman batutuwan tattalin arziki da kuma harkokin kasuwanci.

Exit mobile version