Shugaba Macron Ya Gargadi Turkiya Kan Syria

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya gargadi Turkiya kan ta guji fakewa da farmakin da ta ke kai wa mayakan Kurdawa a arewacin Syria, wajen mamaye wasu daga cikin yankunan ta. Macron ya yi gargadin ne, yayin wata ganawa da ya yi da jaridar Le Figaro, da ake wallafata a Faransa. A makon da ya gabata ne Turkiya ta kaddamar da farmaki ta kasa da kuma sama, kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG da ke iko da yankin Afrin na arewacin kasar Syria.

Turkiya ta na kallon mayakan Kurdawan YPG a matsayin ‘yan ta’adda kuma reshen jam’iyyar kurdawa ta PKK da ta haramta, bayan da PKK din ta dauki makamai tare da ta da kayar baya a yankin kudu maso gabashin Turkiyan shekaru 30 da suka gabata.

Sai dai duk da haka shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana fargaba kan yiwuwar sauya salon farmakin na Turkiya kan Kurdawan zuwa kutsa kai cikin Siriya domin mamaye wasu daga cikin yankunanta, lamarin da Macron ya ce muddin ya tabbata to fa babbar matsala ta auku.

Amurka da Faransa sun jima suna horar da mayakan Kurdawan YPG tare da basu makamai domin taimaka musu wajen yakar kungiyar IS a kasashen Siriya da Iraki.

Exit mobile version