Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja
Shugaban Kasan Nijeriya, Muhammadu Buhari ya dawo gida Nijeriya daga balaguron da yayin zuwa Landan.
Shugaban ya tafi Landan ne daga Birnin New York a ranar alhamis din makon da ya gabata, bayan an karkare taro sashe na 72 na Majalisar Dinkin Duniya, wanda Buharin na cikin shugabannin duniya da suka samu halarta, kuma suka yi fashin baki a taron.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi bankwana da otal din da ya sauka a Birnin New York da misalin karfi 8:05 na safe, inda kuma ya kama hanyar Landan daga filin tashin jirgin sama na JFK.
A daren jiya Litinin ne shugaban ya dawo Nijeriya.