Tun daga shekarar 1999, kwalejin tsakiya mai horar da mambobin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta kan shirya kwasa-kwasai na musamman domin manyan jami’an gwamnatin kasar a farkon kowace shekara, inda shugaba Xi Jinping, kana babban magatakardan kwamitin tsakiyar jam’iyyar, ya kan gabatar da jawabi.
A cikin jawabin da ya yi a kwalejin a shekarar 2016, shugaban ya yi cikakken bayani kan wani sabon ra’ayi na raya kasa, inda ya jaddada cewa, ya kamata a yi amfani da wannan manufa wajen raya kasa da kyau, ta yadda jama’ar kasar za su fahimci darajar manufar.
Shugaba Xi Jinping ya kan tunatar da jami’an gwamnatin kasar Sin muhimmancin jama’a, ya ce manufar gudanar da mulki shi ne, domin kulawa da jama’a. Sa’an nan a wani taron da aka kira a shekarar 2020, shugaban ya bukaci mambobin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da jami’an gwamnatin kasar, su nuna jajircewa da kokarin aiki, ta yadda za su samu kwarewar aiki, da samun nasarori yayin da ake tinkarar wasu kalubaloli. (Bello Wang)