Shugaba Xi Jinping Ya Yi Murnar Saukar Na’urar Bincike Ta Kasar Sin A Duniyar Mars Cikin Nasara

Daga CRI Hausa

Da misalin karfe 7 da minti 18 na safiyar yau Asabar, na’urar binciken duniyar Mars da ake kira Tianwen-1 ta yi nasarar sauka a doron duniyar, al’amarin da ya shaida cewa kasar Sin ta yi nasarar saukar da na’urar bincikenta a duniyar ta Mars a karo na farko. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya daukacin ma’aikatan dake kula da wannan aiki murna tare da jinjina musu.

A sakonsa, shugaba Xi ya nuna cewa, saukar na’urar Tianwen-1 duniyar Mars, muhimmin ci gaba ne da kasar Sin ta samu a fannin binciken sararin samaniya. Wato a karon farko, kasar Sin ta fara gudanar da bincike a duniyar Mars, lamarin dake da muhimmanci ga bangaren binciken sararin samaniya na kasar.

An yi amfani da roka mai lamba LongMarch-5 don harba na’urar Tianwen-1 a ranar 23 ga watan Yulin bara a birnin Wenchang na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, kana ta yi nasarar shiga falakin duniyar Mars a ranar 10 ga watan Fabrairun bana. Sa’annan tun daga ranar 24 ga watan Fabrairun, ta soma kewaye duniyar Mars don gudanar da bincike har na tsawon wata uku, abun da ya aza tubali mai inganci ga sauka a doron duniyar.

Cimmar nasarar saukar da na’urar bincike ta Tianwen-1 a duniyar Mars ta sa Sin ta zama kasa ta biyu a duniya, da ta saukar da na’urar bincikenta a duniyar ta Mars. (Mai Fassara: Murtala Zhang)

Exit mobile version