Wata Kotu a kasar Africa ta Kudu ta zartas da cewa zaben da aka yi wa wani bangare da ke goyon bayan Shugaba Jacob Zuma a kauyen sa shekaru biyu da suka gabata, ya sabawa doka saboda haka an soke.
Hukuncin Babban Kotun da aka zartas a Cape Town na nuna takun saka da ake samu cikin jam’iyar da ke Mulki ANC, wanda zai iya dagula kokarin sa na ganin tsohuwar matarsa Nkosazana Dlamini-Zuma ta maye gulbinsa a matsayin shugaban kasa.
Yankin shugaba Jacob Zuma na KwaZulu Natal da ke gabashin kasar na fama da rikici kuma yankin na da tasiri a wajen zabe a taron kasar na Babbar jam’iyar da ke mulki ANC.