Khalid Idris Doya" />

Shugaban Addini Ya Yi Wa Buhari Hannunka-mai-sanda Kan Ta’addanci

Shugabannin Tsaro

Babban Limamin Masallacin Kofar Dumi dake garin Bauchi, Ustaz Rabi’u Shehu ya shawarci Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya tashi tsaye tare da farkawa daga barcin da ya ke don fuskantar ta’asar da ake yi na salwantar da rayuka da dukiyoyin jama’a a jihohin Barno, Zamfara, Katsina da Sakkwato.

Da ya ke fadakarwa a hudubar sa ta Jummu’a da ta gabata, Shehin Malamin ya bayyana sulwantar rayuka da dukiyoyin jama’a dake faruwa a halin yanzu a jihohin Barno, Katsina, Zamfara da Sakkwato a matsayin abubuwa ne wadanda ba za a lamun ta ba.
Liman Rabi’u Shehu, wanda yayi la’akari da tabarbarewar lamuran tsaro a wadannan jihohin tarayya guda hudu, hadi da kwatanta shi fiye da ta’addancin Boko Haram, da kuma annobar cutar sarkewar numfashi, wato Korona inda gwamnatin tarayya tafi mayar da hankalin ta.
Ya ce abu ne na matukar tashin hankali da jimami, yadda ‘yan ta’adda suke cin karen su babu babbaka a wannan lokaci da manoma suke daura damarar shiga aiyukan gona, yana mai cewar, hana manoma aiwatar da sana’ar su a wannan lokaci yayi banbara-gwai da manufar gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci.
Inji Limamin, “Ta’addanci da aikata wasu manyan laifuka da suke lakuma rayuka da dukiyoyin jama’a wadansu abubuwa ne da suka kasance tamkar ruwan dare a kasar mu. Rayin mutum ya zama tamkar ran kiyashi abin wifintarwa ga shugabanni wadanda suka sha aradun tsare rayuka da dukiyoyin jama’a”.
Shehu ya kuma danganta ta’addanci da ya-ki-ci, ya-ki-cinyewa, kuma ya ke lakume rayukan jama’a yau da kullum tamkar yakin duniya, yana mai gargadin cewar, matukar ba a tashi tsaye an kawar da wannan mujurumanci ba a shiyyoyin arewa maso gabas, da arewa maso yamma ba, lamarin zai wuce sanin ‘yan Njeriya.
Ya kuma danganta abubuwan da suke faruwa a wadannan shiyyoyi biyu na kasar nan da wata mummunar siyasa da ta kasance karan-tsaye wa siyasa, tattalin arziki, walwala da al’adu wa kasashe masu tasowa irin kasar Nijeriya.
Don haka, Malamin ya ce, ya zama wajibi wa Gwamnatin Tarayya ta zage damtse da jan wando, tare da nusar da hukumomin tsaro na kasa domin kawar da wadannan aiyukan bata-gari, kafin wankin hula ya kaimu dare.

Exit mobile version