Daga Mustapha Ibrahim Tela, Kano
Shugaba Trump na Amurka a hirar da ya yi da gidan Rediyon Biafra a wannan mako da ake ciki, ya kalubalanci ’yan kabilar Ibo da cewar, mi ya sa suka ja da baya a fafutukar da suke ta neman Kasar Biafra, zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, a matsayin sa na wanda ya fito daga sashen Kudu. Shugaban ya jaddada cewar yana da masaniyar ko wane sashe yana da dammar samun ‘yancin kanshi, amma zaman kasar Najeriya a dunkule, mafi komai muhimmanci.
Najeriya dai ta samu mulkin kai shekaru 57 da suka wuce, sai dai kuma kabilar Hausa/Fulani sune suka mulki kasar har na shekaru 40, Yarabawa da Ijaw su kuma shekaru 16, su kuma Ibo an barsu da watanni 6. In har Najeriyar daya ce, ai yakamata suma kabilar Ibo, su mulki kasar kamar yadda ko wane bangare ya yi, idan har ana maganar adalci. Kudanci kamata ya yi su mulki Najeriya, kamar yadda Arewaci suka yi.
Gaskiya ne su Ibo kowa ya yi mamakin lokacin mulkin Goodluck sun yi gum da dabin su, sai bayan da Buhari ya kasance shugaban kasa, sai suka tada kayar baya, shi kuma ya bata lokaci wajen daukar mataki, har ga abin yana neman ya kai wankin hula dare. Lokacin yakin neman zabe ai ya je sashen Kudu maso gabas, har ma wani suna su ke kiransa da shi, wato ‘’Okechukwu’’ wannan ya na nuna ke nan ba su dauki shugaban kasa Buhari a matsayin shugaban kasarsu. Wannan ya nuna ken an duk kokarin da ya keyi, bai burgesu.
Shi ma bangaren Arewa duk da ake ganin sun shafe shekaru masu yawa suna mulkin Najeriya, ai suna da nasu matsalolin, da farko ga maganar rashin isashen abincin musamman ga kananan yara, sai maganar annobar ‘’Shan Inna’’, cutar Kuturta, matsalar rashin tsaro, tashe tashen hankula, jahilci, saboda kuwa akwai da akwai yara fiye da milyan 10 wadanda basu zuwa makaranta.
Catalonia al’ummar Barchelona wadda it ace hedikwatar kasar Spain ce, su ma suna neman a raba su da kasar Spain, su samu mulkin kan su, suna daukar matakai wadanda za su kai gas a wa ayi zaben jin ra’ayin jama’a, kamata ya yi su ma shugabannin siyasar Ibo su dauki irin wancan matakin, ba wais u yi ta bugun Kura da gwado ba. Ya ce maganar gaskiya da akwai sauran rina da kaba a Najeriya dalili kuwa, ba isasshen wutar lantarki, har yanzu ana shigo da manfetur daga waje, harkar ilmi da bukatar gyara, hanyoyi mara sa kyau, rashi ayyukan yi, rashin tsaro, shugabanni ba su yin abubuwan da suka dace. Idan kabilar Ibo za su iya samar wa kan su wutar lantarki, ai bai dace sai sun zura ma Abuja ido ba, sai ta kamala rarraba.
‘Yan siyasar Najeriya ba kawai na ‘yan Arewa ba, su kasa samar da kyakkyawan shugabanci ma al’ummarsu, wanda har zai sa su ga an dauke su, su ma an san da zaman su na ‘yan kasa.Idan har ‘yan siyasar suna abubuwan da suka kamata ai, da duk ire iren wadannan tashi tashina ba zata taso ba.