Shugaban CMG Ya Isar Da Sakon Murnar Sabuwar Shekara

A ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2019, ta kafafen rediyo da yanar gizo Mr. Shen Haixiong, shugaban babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), ya isar da sakonsa na murnar sabuwar shekara ga masu sauraro da masu kallo na CMG dake kasashe daban daban, inda yake taya su murnar shiga sabuwar shekara. Mr. Shen Haixiong ya ce, “watsa labaran kasar Sin ga duniya, da watsa labarun duniya ga kasar Sin, tare kuma da inganta fahimtar juna da zumunci a tsakanin al’ummomin kasashe daban daban”, niyya ce ta babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, haka kuma babban aiki ne da ya sanya a gaba. A shekarar 2019, za a cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kuma babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin zai yi kokarin fahimtar da masu sauraronsa da kuma masu kallonsa a kan kasar Sin a sabon yanayin da take ciki. Ga kuma sakon daga Mr. Shen Haixiong.
Ya ku abokai,
A yayin da hasken rana na farko ke kawata duniya a sabuwar shekara, a madadin babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin da ma abokan aikina, ina isar da gaisuwar sabuwar shekara a gare ku, barka da sabuwar shekara!
Yau sama da shekaru 1300 da suka wuce, wani babban mawaki mai suna Wang Bo wanda ya rayu a daular Tang, ya rubuta wata waka da ta shahara sosai a yayin da yake ban kwana da abokinsa malam Du, inda ya ce, “abokin arziki kome nisa yake, nesa ta kan zo kusa”. To, wannan magana ta dace da bayyana abin da na ji a zuci a yanzu.
Ta yiwu wannan ya kasance sabuwar murya a gare ku. Haka ne, a watan Maris na shekarar da ta gabata, a sakamakon irin yanayin da kafofin yada labarai na duniya suka samu kansu a ciki na kara hadewa da juna, an kafa babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, wanda ya hada kan gidan rediyon CRI da gidan talabijin na CCTV da kuma gidan rediyon CNR. A lokacin, Ricardo Huerta, da ya zo daga kasar Argentina, ya rubuta a shafin sada zumunta cewa, “Ina taya babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin murnar kafuwa, wanda ya fahimtar da ni a kan kasar Sin kyakkyawa, wanda kuma ya fahimtar da ni a kan karfin zumunci.”
Ina godiya da kwarin gwiwar da abokanmu tsoffi da sabbi suka ba mu, wadanda suka ba mu kwarin gwiwar da a ko da yaushe za mu iya tunawa a zukatanmu. Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin da aka kafa yana daukar nauyin watsa labarun kasar Sin zuwa ga kasashen duniya, da watsa labarun duniya ga kasar Sin, tare kuma da inganta fahimtar juna da zumunci a tsakanin al’ummomin kasashe daban daban. Muna fatan za mu kara inganta aikinmu tare kuma da gamsar da ku.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, “Ba a iya raba ci gaban kasar Sin da duniya, haka kuma ba a iya raba ci gaban duniya da kasar Sin.” a cikin shekarar da ta gabata, mun yi kokarin inganta mu’amala a tsakanin kasar Sin da kasashen duniya, inda rahotannin da muka samar dangane da cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da bikin baje kolin kayayyakin da kasar Sin ke shigowa da su (CIIE) a karo na farko, da taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka (FOCAC), sun jawo hankalin al’umma, inda kuma muka kare adalci a kokarin da aka yi na kiyaye ‘yancin yin ciniki da dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya, mun yi ta fito da muryar kasar Sin a taron kolin APEC da na G20. Baya ga haka, mun kuma yi kokarin hada kasar Sin da sauran kasashen duniya bisa ga jerin manhajojin da muka samar, wadanda suka hada da “kanun labaran Sin da Rasha” da “CINITALIA” da “mu’amalar Sin da Japan”, da “CMG Español” da sauransu, kuma a kokarin da muka yi na tuntubar kasashen duniya, mun kuma kira babban taron kafofin yada labarai na kasashen Asiya karkashin dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Bo’ao, da kuma taron kafofin yada labaran hada-hadar kudi da tattalin arziki da ma kwararu na kasa da kasa na Hongqiao, wadanda suka jawo hankalin kafofin yada labaran duniya. Banda haka kuma, ayyukan da muka gudanar da suka hada da “samar da fina-finan kasar Sin a Afirka”, da “wasannin kwaikwayon kasar Sin” da na “ni mai sha’awar kasar Sin ne” sun kara jawo karin mutane masu sha’awar kasar Sin.
A wannan sabuwar shekarar da muka shiga, za a cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama’ar Sin. Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin zai yi kokarin fahimtar da masu sauraronsa da kuma masu kallonsa game da kasar Sin a sabon yanayin da take ciki. A cikin sabuwar shekara, za mu gabatar da jerin shirye-shirye masu inganci da za su burge ku, za mu kuma bayyana yadda “kasar Sin ke kiyaye zaman lafiyar duniya da ba da taimako ga ci gaban duniya da kuma kiyaye tsarin doka da oda a duniya.” Za mu kuma yi kokarin kirkiro sabbin hanyoyin yada labarai, za mu yi amfani da sabbin fasahohin da suka hada da fasahar sadarwa ta 5G, babbar ma’ajiyar tattara bayanai, samar da bayanai ta yanar gizo, da dai sauransu, za mu yi kokarin zama kafar yada labarai ta zamani wadda za ta zamo a sahun gaba a duniya.
Tsohon abokinmu na kasar Rasha Yuri Tavrovsky, wanda ya rubuta littafin nan mai taken: Xi Jinping: Cimma Mafarkin Sinawa, ya taba aiko mana cewa, “Na gaskanta cewa, al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da kasar Sin ta gabatar, wata fitila ce da za ta nuna mana hanya a yayin ci gaban kasashen duniya.” Haka ne, duniya daya ce ga bil Adam baki daya, haka kuma duniya daya ce ga kasa da kasa. Bari mu kokarta domin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama da samar da zaman lafiya mai dorewa da tsaro da albarka a duniya!
Gaisuwa a gare ku, mun gode!
(Mai fassara:Lubabatu Lei)

Exit mobile version