Shugaban kasar jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, Felix Tshisekedi, ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi wanda ke ziyarar aiki a Kinshasa.
Tshisekedi ya ce, DRC ta yabawa taimakon da kasar Sin ke ba ta wajen yaki da annobar COVID-19 da kuma tallafawa cigaban tattalin arzikinta.
Shugaba Tshisekedi ya ce, nan ba da jimawa ba, kasarta za ta karbi ragamar shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afrika AU, kuma a shirye take ta shiga a dama da ita a hadin gwiwar Sin da Afrika kuma tana maraba da karin kamfanonin kasar Sin su zuba jarinsu a kasarta, kana kasarta tana son karfafa hadin gwiwa da Sin a fannin samar da ayyukan more rayuwa da sauran fannoni.
A nasa bangaren, Wang Yi ya ce, mu’amallar tallafawa juna da mutunta juna wata muhimmiyar al’ada ce a tsakanin Sin da DRC. Kasar Sin ta yabawa kokarin gwamnatin DRC na daukaka matsayin kyakkyawar dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da DRC kuma tana burin cigaba da kasancewa sahihiyar aminiyar hadin gwiwar DRC a dogon lokaci. (Mai fassara: Ahmad)
Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Duba Marasa Lafiya Sama Da 4,000 A Ghana A 2020
Tawagar jami’an lafiya ta kasar Sin kashi na 9 dake...