Shugaban Gudanarwar Arsenal Ya Fi Son Arteta Ya Maye Gurbin Wenger

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Ivan Gazidiz, kuma wanda ya fi kowa hannun jari mafi yawa a kungiyar ya bayyana ra’ayinsa cewa ya fi son tsohon dan wasan kungiyar, Mikel Arteta ya maye gurbin Wenger a kungiyar.

A ranar Juma’a ne dai Arsene Wenger ya bayyana cewa zai ajiye aikinsa na koyar da kungiyar idan kakar wasa ta kare, bayan da ya shafe shekaru 22 yana aiki da kungiyar inda ya lashe kofin Firimiya guda uku da kofin kalubale guda bakwai.

Tun a ranar ne dai aka fara bayyana sunayen wadanda ake tunanin za su maye gurbin nasa a kungiyar ciki har da tsohon mai koyar da ‘yan wasan Barcelona, Luis Enrikue da tsofaffin ‘yan wasan kungiyar, Patrick Biearra da Thierry Henry da kuma Mikel Arteta

Sai dai an bayyana cewa shugaba Gazidiz ya fi son Arteta ya maye gurbin na Wenger a Arsenal saboda kwarewarsa ta buga gasar firimiya sannan kuma shi ne mataimakin mai koyar da ‘yan wasan Manchester City, Pep Guardiola wadanda suka lashe gasar Firimiya ta bana.

Arteta, mai shekara 36 ya buga wasanni 149 a kungiyar ta Arsenal sannan kuma ya zura kwallaye 16 cikin wasannin da ya buga wa kungiyar, sannan kuma kafin Arsenal ya taba buga wa kungiyar kwallon kafa ta Everton wasa

Exit mobile version