Shugaban Hukumar JAMB Ya Kalubalanci Manyan Nijeriya

Daga Muhammad A. Abubakar

Rijistiran Hukumar Shirya Jarabawar Sharar Fage ta shiga Jami’a ‘JAMB’, Ishak Oloyede ya shawarci manyan kasa da su rika saka wadanda suke daukar dawainiyyarsu suna digirinsu na farko a kasarsu kafin su fita zuwa kasashen waje.

Oloyede wanda ya bayar da wannan shawarar a ranar Juma’ar makon da ta gabata a lokacin da yake hira da manema labarai a wani taro na musamman dangane da samun horo da saka kula dangane da bin hanyoyin da suka dace wajen bayar da gurbin karatu a Jami’a, na zangon karatun shekerar 2017/18.

Kamar yadda ya bayyana, ya ce; abu ne mai matukar muhimmanci ya zama ’ya’yansu sun sami digirinsu na farko a kasarnan, inda ake da jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu wadanda suke da inganci da nagarta fiye da su kai su Jami’o’in kasashen waje wadanda ba su da inganci da nagarta.

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, wato FRSC ta bayyana cewa; mutane 423 ne suka rasa rayukansu a ya yin da mutum 2, 339 suka jikkata a sakamakon hadarin mota guda 768 da suka auku a fadin kasarnan a watan Yuli kawai.

Hukumar ta bayyana haka ne a rahotonta na wata-wata a lokacin da ta fitar da na watan Yuli wanda ta aikewa kamfanin Dillancin Labarai na kasa a Abuja a ranar Juma’a.

Rahoton wanda Shugaban Hukumar, Boboye Oyeyemi ya sakawa hannu ya bayyana cewa; a watan Yulin, an samu karuwar rasa rayuka fiye da na watan Yuni da adadin mutane 122 wanda ya dauki kashi 41. Ya ci gaba da cewa; a watan Yuni an samu hadurra 738 ne a duk fadin kasar wanda ya ci rayukan mutane 301, mutane 2, 157 kuma suka jikkata.

Rahoton baya-bayan nan ya tabbatar da cewa; hadurran da suka auku da adadin wadanda suka raunata a watan Yuli idan aka kwatanta da na watanni baya za a ga na watan Yulin adadin mutanen ya karuwa ne da 30 ko 182 wanda yake daukar kashi 4 da kuma kashi 8 cikin dari.

Birnin tarayya Abuja ya ci gaba da rike kambunsa a matsayin na farko wajen samun yawan hadurra fiye da kowanne Jihohi 36 da ake da su a kasarnan, a inda aka samu rahotannin hadura 93 wanda suka yi sanadiyyar mutuwar 17 da jikkata 167 a watan Yulin.

Jihar Kaduna ita ce ta zo ta biyu a yawan samun hadurra, inda aka samu hadurra 54 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 43 da jikkata mutane 198. Sai Jihar Neja wacce ta zo ta uku, inda aka samu rahotannin hadurra 48 wanda suka ci rayuka 24 da jikkata 148. Kamar yadda rahoton ya bayyana.

Rahoton ya ci gaba da cewa; jihohin da aka samu munanan hadurra wanda ya ci rayuka, Jihar Kaduna ce akan gaba, inda mutane 43 suka rasa rayukansu. Sannan Jihar Ogun da ya ci rayuka 33, sai jihar Jigawa inda mutane 27 suka rasa rayukansu. Har wala yau Jihar Osun ce ta biyo su a baya, inda mutane 26 suka rasa rayukansu, sannan sai Jihar Neja inda mutane 24 suka rasu sakamakon hadurra. Jihar Kogi hadarin ya ci rayuka 22, sannan sai jihar Ebonyi inda mutane 20 suka rasa rayukansu duk a sakamakon hadurra.

Rahoton ya bayyana cewa; gudun wuce ka’ida wanda ya sabawa dokokin hukumar a hadurra 505 shi ne ya kwashi kashi 56.4 a watan Yulin, ya ce; wannan yana daga cikin abubuwan da suke haifar da hadurran. Sannan tukin ganganci wanda ya debi kaso 85 zuwa 9.5. Har wala yau an samu rahotanni 57 na fashewar taya na hadurran da suka auku wanda ya wakilci kashi 6.4. Sai oba-tekin na ganganci wanda ya debi kashi 52 ko 5.8 na dukkan hadurran da suka auku.

Rahotan ya tabbatar da cewa; adadin abin hawa 1, 257 ne suka samu hadurra a watan Yulin, a inda guda 738 wanda ya debi kashi 58.7 duk na haya ne. Motoci 499 wanda ya wakilci kashi 39.7 motocin gida ne. Sai kuma guda 20 na gwamnati ne. Rahoton yana dauke da wata a takarda a bayansa zuwa ga Sakataren gwamnatin tarayya wanda Ofishinsa ke sakawa Hukumar ta FRSC ido.

A cikin wasikar, Shugaban Hukumar ta FRSC ya roki taimakon kara tallafa musu da kayan aiki, wadanda zasu rika kula da gudun wuce ka’ida, musamman radar wanda zai taimaka musu wajen gane masu gudun wuce ka’ida daga direbobi.

Exit mobile version