Shugaban Ilimi Na Bai-ɗaya Ya Ja Kunne Malamai A Katsina

Daga Sagir Abubakar, Katsina

Daraktan kula da sashen mulki na Hukumar ilimin bai-ɗaya ta Jihar Katsina, a ziyarar da ya kai makarantu ya umurci hedimastoci da su kai rahoton duk wani malamin makaranta da ya ƙi zuwa wurin aiki akan lokaci. Alhaji Halliru Duwan ya bada wannan umurnin ne lokacin da ya ziyarci wasu makarantun firamare a Ƙaramar Hukumar Mani.

Bugu da ƙari ya ja hankalin malaman makarantar da su guji ƙin zuwa wajen aiki ko zuwa a makare, da kuma tashi kafin lokaci. Shugaban na sashen mulki ya ce gwamnatin jiha mai ci yanzu ta bada fifiko ga ɓangaren ilmi musamman ilmin firamare.

Advertisements

Daga cikin makarantun firamare da aka ziyar ta sun haɗa da na garin Muduru, Sheme, Bagiwa da Muhammad Dikko, ganin irin yadda wannan gwmanatin da ke kan karaga yanzu ta dukufa wajen haɓaka  ilmi a ciki da kewayen jihar nan, gwamna Aminu Bello Masari ya nuna cewa dukan wani malami ko wani jami’i wanda abin ya shafa idan aka same shi ya na wasa da aikin sa to haƙiƙa gwamnati ba za ta saurara masa ba.

Gwamnan ya ƙara bada fifiko akan cewar duk wani shugaban makaranta da jami’ansu,  su sani wannan gwmanati ba za ta lamunci wasa ko yi ma aiki riƙon sakainar kashi ba, tilas malamai su sa himma wurin aikinsu.

Exit mobile version