Nasir S Gwangwazo" />

Shugaban Jaridun Manhaja Da Blueprint Ya Sabunta Rajistarsa Ta APC

Shugaban kamfanin buga jaridun Manhaja da Blueprint, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya sabunta rajistar sa ta zama dan jam’iyyar APC a rumfar zaben sa da ke Malagi, a karamar Hukumar Gbako da ke Jihar Neja.

Bayan ya kammala rajistar tasa a ranar Juma’a, Alhaji Idris ya yaba da yadda aikin yin rajistar ke gudana cikin lumana a rumfar zaben su, sannan ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC a fadin jihar da kowa ya tabbatar da ya yi rajista ko sabunta rajistar sa.
Ya ce, “Na yi matukar farin ciki da yadda aikin yin rajistar ke gudana. Wannan wata alama ce mai nuna yadda ‘yan jam’iyyar da ma masu sha’awar shigar ta ke da burin bunkasa jam’iyyar da ma dimukradiyya a jihar.
“Don haka na ke kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar da ma masu sha’awar su shige ta a jihar da kowa ya je ya yi rajista.”
Alhaji Idris, wanda har wa yau shi ne shugaban kamfanin Bifocal Group da gidan rediyon WeFM da ke Abuja, ya ce ya yi koyi ne da Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani-Bello da dukkan shugabannin APC na ciki da wajen Neja, wadanda su ka riga su ka yi tasu rajistar a wurare daban-daban, wajen sabunta rajistar sa.
Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihar da su rika shiga ana damawa da su a harkoki a matakin jiha da kasa maimakon su zama ‘yan kallo.
A cewarsa, “Wajibi ne mu hada hannu wajen ciyar da tsarin dimukradiyy a Nijeriya gaba, mu gina al’ummomin mu, jihar mu da ma kasa baki daya ta hanyar shiga ana damawa da mu, amma ba mu zama ‘yan a bi yarima a sha kida ba.
Jigon ya yaba wa Shugaba Buhari da kuma Gwamna Bello bisa yadda su ka sakar wa kowa mara don tsofaffi da sababbin ‘yan jam’iyyar kowa ya yi rajistar sa ba tare da wata takura ba.
Daga bisani ya shawarci jama’a da su kiyaye dukkan dokokin yaki da korona da aka shimfida yayin yin rajistar domin taimaka wa kokarin gwamnati wajen yaki da cutar.
A karshe, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya yi godiya ga dukkan wadanda su ka yi masa rakiya zuwa wajen sabunta rajistar sa  wadanda su ka hada da shugabannin APC na yankin da abokan hulda da magoya bayan sa.

Exit mobile version